Asibitin Gwamnati a Saudiyya ya caji ’yar kasa Naira miliyan 24

Wani asibitin gwamnati a qasar Saudiyya ya caji wata ’yar qasar Riyal dubu 400, wato daidai da Naira miliyan 24 a matsayin kudin maganin mahaifinta, kamar yadda wata jaridar qasar ta ruwaito.  Asibitin da ake kira Al-Noor Speacialist Hospital, Daraktansa, Dokta Ayman Yamani, ya ce ma’aikatar lafiya ta qasar tana daukar dawainiyar kula da lafiyar […]

Asibitin Gwamnati a Saudiyya ya caji ’yar kasa Naira miliyan 24
Asibitin Gwamnati a Saudiyya ya caji ’yar kasa Naira miliyan 24

Wani asibitin gwamnati a qasar Saudiyya ya caji wata ’yar qasar Riyal dubu 400, wato daidai da Naira miliyan 24 a matsayin kudin maganin mahaifinta, kamar yadda wata jaridar qasar ta ruwaito. 

Asibitin da ake kira Al-Noor Speacialist Hospital, Daraktansa, Dokta Ayman Yamani, ya ce ma’aikatar lafiya ta qasar tana daukar dawainiyar kula da lafiyar ’yan qasa ne kawai.
“’Yar majiyacin ’yar Saudiyya ce, amma mahaifinta asalinsa dan nahiyar Asiya ne. Ya kwanta a wannan asibiti tsawon watanni biyar da suka wuce, bayan raunin da ya samu a wani hadarin mota. Kuma majiyacin bai san inda kansa yake ba, shi ya sa aka yi ta kula da shi, a sashen bayar da kulawa ta musamman,” inji Yamani.
Jami’in hukumar ya ce, majiyacin wanda tsoho ne bai nuna alamun samun sauqi ba, don yana buqatar ci gaba da zama a asibitin na tsawon wani lokaci
“Ayyukan kula da lafiyar da asibitin ke yi ba kyauta ba ne. Su kansu ’yan qasar qungiyoyin taimako da hukumomin da ke qarqashin ma’aikatar lafiya ke biya musu kudin magani. Shi ya sa idan al’amari ya shafi wadanda ba ’yan Saudiyya ba, ma’aikatar na biya wasu kudin, amma ba a kodayaushe ba.
Ya bayyana cewa, dole ne ’yar majicin ta biya kudin asibitin, ko kuma a qi ba ta mahaifinta, sannan kudin kula da lafiyarsa za su ci gaba da qaruwa.
Ita kuwa ’yar majiyacin, wace shekarunta 35, cewa ta yi, mahaifinta dan shekara 65 yana cikin wani mawuyacin hali.
“An shafe wata biyar halin da mahaifina ke ciki sai qara tsananta yake yi. Don haka ba zan iya biyan Riyal Dubu 400, tun da har yanzu mahaifina yana buqatar qarin kula da lafiyarsa. Hukumar asibitin ta shawarce ni idan na nemi taimako daga qungiyoyin jinqai, wadanda za su iya biyan kudin maganin,” injita.
Ta ce, ta samu taimako wani kason kudi daga cibiyar bayar da kula, al’amarin da zai ba ta dama ra yi mata magani a asibiti kyauta. Sai dai asibitin sun qi amincewa ta yi amfani da wannan tallafin kason kudin magani.
“Na yi qoqarin amfani da tallafin ga mahaifina, amma asibitin ya qi amincewa. Sun ce tallafin an bayar da shi ne ga ni ’yar Saudiyya ba mahaifina ba. Don haka ban san yadda zan biya wadannan kudi da ake buqata ba,” a cewar ’yar majiyacin da ke cike da damuwa.