Asibitin intanet ke duba lafiyar mutanen Sin
Asibitin da likitoci ke ganawa da marasa lafiya ta shafukan intanet na habaka a kasar Sin, inda rayuwar mutanen kasar ta inganta a fannin kula da lafiya. Sai dai masana sun ce akwai kalubale a tattare da irin wadannan cibiyoyin kula da lafiya na zamani ba.Ranar da Zhang ya samu magungunan shawo kan hawan jinni […]
Asibitin da likitoci ke ganawa da marasa lafiya ta shafukan intanet na habaka a kasar Sin, inda rayuwar mutanen kasar ta inganta a fannin kula da lafiya. Sai dai masana sun ce akwai kalubale a tattare da irin wadannan cibiyoyin kula da lafiya na zamani ba.
Ranar da Zhang ya samu magungunan shawo kan hawan jinni a gidansa, sai ya samu saukin kai kawo wajen tuntubar likita. Sashen kula da lafiya da ke cikin intanet, wani sabon fanni ne na likitanci da ya bambanta da tsarin al’ada da aka saba amfani da shi, al’amarin da ke habaka a kasar Sin cikin wakdannan shekaru.
“Na saba ganawa da Dokta chen a Asibitin Ningbo daga lokaci zuwa lokaci,” inji zhang. Ya fara gajiya da ziryar ganin likita da kimanin karfe biyar na yamma, inda yak an hau motocin bas biyu, sannan ya bi layin ganin Dokta Chen.
Zhang dai ba shi kadai ba ne ya amfana da giza-gizan ganin likita a asibitin Ningbo da ke intanet a kasar Sin ba. Mutane irin su He Minhdao dan shekara 68, ya samu damar ganawa da kwararren likita ta intanet, ko a lokutan da yake tare da likitoci a karamin asibitin kula da lafiyar al’umma, ta hanyar amfani da giza-gizan sadarwar asibiti.
Giza-gizan sadarwar Ningbo da ke asibitin “Ningbo Cloud Hospital,” an fara aiwatar da wannan tsarin kula da lafiya ne cikin watan Maris din barta. Kuma giza-gizan sadarwar kula da lafiya na Ningbo sun zama hadaddun likon alakar asibitocin yankin da mazauna karkara. Sannan akwai gini na musamman da aka kebe don ganawa da likitocin asibitin.
Marasa lafiya na iya smaun ganawa da likita ta hanyar bidiyo, a yi nazarin cutar su, a ba su magani, duk ta shafin intanet; kodayake ana iya aike musu da magunguna har gidan su. Sannan suna iya zuwa kwaramin asibiti mafi kusa da su kafin su samu ganawa da manyan likitoci ta shafunkan intanet.
Ningbo dai ta zama wata katafariyar cibiyar kula da lafiya. Sannan cibiyar ta samar da asibitoci a biranen da suka hada da Hangzhou da Guangzhou da Wuhan da ke gudanar da ayyukan su ta shafuklan sadarwar intanet. Cibiyoyin kula da lafiya sun yi karanci a kasar Sin, indak ashi 70 cikin 100 suke a birane, a cewar Sun Yang, mataimakin daraktan harkokin mulki a sashen kula cibiyar kula da lafiya da ke karkashin Hukumar Lafiya da tsara iyali ta kasa; hukumar da ke da alhakin sa’ido kan harkokin kula da lafiya, kamar yadda yake kunshe a rahotonta na shekarar 2012. Jaridar The Telegraph Uk da Chinadaily suka baza wannan labara a duniya.