Asibitin Kano mai shekara 106 da ke da likita 1 kacal
Zahirin halin da Babban Asibitin Yadakunya da aka fi sani da Bela a Kano ke ciki
Kaddara wannan lamarin a zuciyarka, babban asibiti tilo a karamar hukuma mai mutane fiye da dubu 400, amma likita daya ne mai duba marasa lafiya.
Bayan nan, babu sashin ba da agajin gaggawa idan an samu hadari, babu tsaftataccen bandakin da marasa lafiya da masu jinya za su kewaya, ba kuma ruwa da wutar lantarki.
- Dan sanda ya kashe abokin aikinsa a Kebbi
- An cafke wani mutum da katunan zaben jama’a a Sakkwato
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sauya Takardun Naira Za Ta Shafe Ku
Abin ya yi maka kamar almara ko?
Zahirin halin da Babban Asibitin Yadakunya da aka fi sani da Bela a Kano ke ciki ke nan.
A ziyarar da Aminiya ta kai asibitin ta iske tarin matsaloli da asibitoci da dama a jihar ke fama da su, har ma da kari jibge a cikinsa, domin baya ga wadancan matsaloli da muka zayyana, babu isassun ma’aikatan lafiya da wutar lantarki, hadi da dakuna da makewayi lafiyayye kuma tsaftatacce.
Haka sadarwar waya na da wahalar samu da zarar ka shiga cikin asibitin, wanda babban kalubale ne ga kiran gaggawa daga ciki ko wajen asibitin.
Wata majinyaciya da Aminiya ta tarar a asibitin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce tunda aka kwantar da danta a asibitin, ba ta taba samun ruwan da za ta yi amfani da shi ba a cikin asibitin.
“Ni dai kin ga gaskiya tunda na zo asibitin nan ban taba samun ruwa a cikinsa ba, sai dai in fita in debo a waje ko in sayi na leda.
“Babu kuma wutar lantarki, ban-daki kuma akwai, amma fa a lalace yake ga kazanta,” in ji ta.
Ban-dakunan da Aminiya ta gane wa idonta, ta tarar da su a lalace, wasu kuma cike suke da kwata, wasu kuma dabensu a farfashe yake, sannan babu ruwa.
Wani ban-daki guda daya da ke rufe kuma, bayanai na nuna Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Alhaji Garba Ramat ne ya gina shi ba da jimawa ba.
Asibitin da ya cika shekara 106 da kafawa, a baya ya shahara ne wajen magance cutar kuturta da sauran cututtukan fata.
Sai dai yanzu gwamnati ta mai da shi babban asibiti.
Alhaji Murtala Bashir shi ne Mai garin Yadakunya, garin da asibitin yake, ya bayyana wa Aminiya cewa kasancewar asibitin mai dadadden tarihi, mutane kan yi matukar mamaki idan suka shiga suka ga halin da yake ciki.
“Magana ta gaskiya asibitin nan na fama da dimbin matsaloli kwarai da gaske, na san ke ma kin ga wasu da idonki.
“Ba mu da wutar lantarki, sai da inji ake kunnawa.
“Gwamnati ce ke aiko da man da ake zuba masa a tashe shi, amma yanzu ba a cika kawo shi kamar baya ba.
“Hakan ya sa sai dai mu zabi lokutan kunna shi, ko mu zuba mai da kudinmu musamman da daddare,” in ji shi.
‘Har daga kasashen waje ana kawo marasa lafiya’
Ya kara da cewa: “Kada ki manta asibiti ne yanzu babba da har haihuwa muna karba, ga kuma marasa lafiya har da kasashen ketare irin su Nijar da Ghana da Chadi ana kawo mana.
“Idan kika dawo gida Najeriya kuma babu jiha a Arewacin Najeriya da ba a kawo mana marasa lafiya.
“Sannan mu a nan Karamar Hukumar Ungogo wajen garuruwa 100 da ke kewaye da mu nan suke zuwa idan ba su da lafiya.”
Likita daya, karancin ma’aikata
“To fa duk wannan lissafin da na yi miki kuma, likita daya yake duba su.
“Baya ga likita kuma sauran ma’aikatan lafiyar babu wadatattu,” in ji shi.
Don haka Alhaji Bashir ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa-da-tsaki, su kai musu dauki, duk da suna da masaniyar kokarin da ta yi kan asibitin.
“Kin ga gwamnatin baya ta Injiniya Rabi’u Musa Kwanakwaso ce ta sabunta gine-gine da yawa na asibitin, sai gwamnati mai ci ta Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta kewaye mana asibitin, domin da a bude yake ta ko’ina za ka iya shigowa.
“Wannan kewayewa ta taimaka wa tsaron asibitin sosai, amma akwai bukatar kari, saboda yanzu asibiti ne babba da har da unguwar ma’aikata a ciki,” in ji shi.
Dambarwar sakacin likitoci a Kano
Idan za a iya tunawa a baya-bayan nan Jihar Kano ta cika da samun korafe-korafe daga mutane kan yadda ma’aikatan lafiya ke sakacin da ake samun mutuwar marasa lafiya, baya ga kyara.
Sai dai da alama masu gudanar da Asibitin Bela na kokarin ware kansu daga wancan rukunin, inda suke rage matsalolin asibitin ke fama da su.
Wannan kokari nasu ne ma ya kai su ga kafa wani kwamiti da ya kunshi mazauna yankin, inda suke duba matsalolin asibitin, su kuma yi kokarin warware su a tsakaninsu.
“Wata biyu da suka wuce Daraktan Shiyya da asibitin ke karkashin kulawarsa, Dokta Abdullahi Isma’il Kwalwa, ya jagoranci kafa kwamitin, kuma ni ma a matsayina na mai unguwa ina cikinsa.
“Kuma a karkashin kwamitin muna warware kananan matsaloli da dama, domin da shi ne yanzu muke kokarin kawar da masu shigowa asibitin nan suna janye marasa lafiya daga sayen magani a ciki.
“Kasancewar mun san su don ’yan unguwar ne, muna kokarin samar da hanyar da za a rage matsalar, ya zama sai idan namu ya kare ne sannan za a je waje a saya, bayan mun tantance ingancin maganin,” in ji mai garin.
Bukatar sashen ba da agajin gaggawa
Daga nan ya roki gwamnatin jihar ta samar musu da sashen ba da agajin gaggawa, domin asibitin ya amsa sunansa na babban asibiti.
Babu kan famfuna —Hukumar Asibitin
Yunkurin jin ta bakin hukumar hudanarwar asibitin kan matsalolin ya ci tura, domin sakataren asibitin ya ce ba ya da hurumin yin hakan, sai ya karbo izini daga na gaba da shi.
Sai dai wani babban jami’i da ya nemi a sakaya sunansa a cikin masu ruwa-da-tsaki wajen gudanar da asibitin, ya ce batun babu ruwa a asibitin ba gaskiya ba ne, kan famfuna ne babu.
Ya ce, “Bohol uku gwamnati ta samar mana, kuma akwai tankin da inji ke jan ruwan ya kai cikinsa.
“Amma sai dai ka je har sashin haihuwa inda tankin yake, sannan za ka diba.
“Batun karancin ma’aikata a sibitin ma gaskiya ne likita kwalli daya ne a asibitin, sai ma’aikatan jinya 17, da na sashin ba da magani shida da masu gwaji biyar.”
“Idan kika duba yawan masu zuwa asibitin za ki ga aikin ya yi musu yawa, kuma a haka ma ba mu da sashin ba da agajin gaggawa, yaya kike gani idan aka samar da shi ba tare da an karo wasu ba?
“Kina gani fa ko rigar ma’aikatan jinyar nan babu ma’aikacin da ke sanyawa, ai kin san ana bukatar dauki,” in ji shi.
Mun kafa kwamitin bincike – Gwamnati
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mu’azzam, ya ce tuni hukumar ta kafa kwamitin da zai ziyarci asibitin domin binciko matsalolin da yake fama da su da nemo hanyoyin magance su.
A lokacin rubuta labarin, Aminiya ta samu labarin kwamitin ya ziyarci asibitin kamar yadda hukumar ta bayyana, sai dai a jira a gani ko za a dauki matakin da ya dace.