Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Hakan zai rage yawaitar shigar miyagun mutane cikin asibitin.

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Asibitin Malam Aminu Kano

A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin.

Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su iya shiga, amma sai an bi ka’idojin tsaro na musamman.

A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar, ya ce, an kafa dokar hana motocin masu baƙin gilashi shiga ne saboda wasu munanan abubuwan da suka faru.

Ya bayyana irin munanan ababen kamar yunƙurin sace mutane ta amfani da irin waɗannan motocin da kuma aikata ayyukan laifi daban-daban da suka ƙunshi sata da aikata abubuwan da ba su dace ba a cikin harabar asibitin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ma’aikatan asibitin da ke amfani da mota za su yi rajistar motocinsu a ofishin tsaro don samun tambarin tantancewa da izinin shiga.

A cewar rahotanni, satar motoci da babura da sauran kayayyaki masu daraja ta yi yawa a cikin harabar asibitin.

Haka kuma, an gano cewa, wasu mutane na amfani da harabar asibitin wajen aikata ayyukan ashsha, wanda hakan ya sa mahukuntan suka ɗauki wannan mataki na hana motoci masu baƙin gilashin shiga, don kare rayukan ma’aikata da marasa lafiya da baki.

Wani ɗalibi mai suna Ahmad Bala, wanda ya zo asibitin da mota mai baƙin gilashi, an dakatar da shi daga wurin jami’an tsaron da ke bakin ƙofa.

Ya ce, wannan doka tana da amfani, amma ya buƙaci a cire dalibai daga dokar.

“An dakatar da ni saboda baƙin gilashi, amma ni ɗalibi ne kuma ina goyon bayan wannan mataki.

“Amma ina ganin ya kamata a cire ɗalibai daga wannan doka saboda wannan asibitin koyarwa ne, kuma ɗalibai da dama suna zaune a cikin harabar asibitin,” in ji Bala.

Shugaban tsaro na asibitin, Sani Ahmad Mahmud ya bayyana cewa, matakin hana shigar motoci masu baƙin gilashin yana cikin manufofin kare ma’aikata da marasa lafiya da baƙi da ke zuwa asibitin.

“Wannan mataki ya zama wajibi saboda ƙalubalen tsaro da muke fuskanta. Ina kira ga jama’a su bi wannan doka tare da girmama ta, domin matakin yana cikin muradinsu,” in ji Mahmud.

Wasu daga cikin jama’a sun yaba da matakin, suna ganin hakan zai rage yawaitar shigar miyagun mutane cikin asibitin, inda suke amfani da damar babban harabar wajen aikata laifuka da ayyukan da ba su dace ba.

Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu