Asibitin Malam Aminu ya yi gwajin cutar daji kyuta ga mata

daruruwan mata sun amfana da gwajin cutar daji da Asibitin Malam Aminu Kano ya gudanar a bikin makon cutar daji ta duniya da aka gudanar a Kano.Makon bikin cutar dajin lokaci ne da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kebe duk shekara don tunatar da mata a kan muhimmancin gwajin lafiyarsu game da cutar dajin […]

Asibitin Malam Aminu ya yi gwajin cutar daji kyuta ga mata
Asibitin Malam Aminu ya yi gwajin cutar daji kyuta ga mata

daruruwan mata sun amfana da gwajin cutar daji da Asibitin Malam Aminu Kano ya gudanar a bikin makon cutar daji ta duniya da aka gudanar a Kano.
Makon bikin cutar dajin lokaci ne da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kebe duk shekara don tunatar da mata a kan muhimmancin gwajin lafiyarsu game da cutar dajin mama da ta mahaifa da ta mafitsara. Haka makon kan mayar da hankali wajen ceto rayukan miliyoyin jama’a a duniya ta hanyar fadakarwa da ilimintar da su a kan cutar daji da neman hadin kan gwamnatoci da kungiyyoyi da daidaikun mutane a kokarin magance cutar a duniya.
Gwajin wanda kyauta ne an dauki tsawon kwana uku ana gudanar da shi a asibitin, inda aka gwada lafiyar mata a kan cutar dajin mama da ta mahaifa da ta mafitsara da ta fi addabar maza.
Shugaban Sashin Fida na Asibitin Dokta Abdurrahman Mahmud Sheshe ya bayyana wa Aminiya cewa tun farko hukumar asibitin ta yanke shawarar gudanar da gwajin ne saboda la’akari da yadda cutar ke karuwa a tsakanin al’umma.
Dokta Abdurahman Sheshe ya ce rashin gano cutar a kan lokaci ne ke haddasa yaduwar cutar. “Shi ya sa yana da kyau mutum ya rika duba kansa da kansa ko kuma ya zo asibiti a duba shi don a gano ciwon da wuri. Hakan zai sa mutum ya samu magani yadda ya kamata, idan an duba cutar a kullum karuwa take a tskanain al’umma,” inji shi.
Wani kwararren likitan mata da ke asibitin Dokta Umar Usman ya ce “Dalilan da suke jawo cutar suna da yawa; wani lokaci akan samu kansar da kwayoyin cuta ke kawo ta, akwai kuma na gado, akwai wadanda suke samuwa ba a san dalilin faruwarsu ba. Yawanci kansa na samuwa ne a maimakon kwayoyin halitta su rika raguwa bisa ka’ida sai ya zama cewa girmansu da rarrabuwarsa su yi ta yaduwa ba bisa ka’ida ba.”
Dokta Usman ya ce mayar da hankali akan gwajin lafiya kan taimaka wajen gano alamomin cutar da kuma hanyar magance ta a kan lokaci.
Malama Amina Muhammad Hotoro tana daga cikin wadanda suka amfana da wanann gwaji ta bayyana wa Aminiya cewa ta zo asibitin ne don a gwada lafiyarta kasancewa ciwon sankarar na barazana ga jama’a.