Asibitocin Abuja za su fara amfani da POS
Ya ce wannan matsala ba a iya Abujan ta tsaya ba.
POS
Hukumar Birnin Tarayya (FCTA) ta bai wa asibitoci umarnin fara amfani da na’urar POS don saukaka wa marasa lafiyar da ba su da tsabar kudi a hannu.
Sakataren lafiya na hukumar, Dokta Abubakar Tafida ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Abuja.
- Buhari ne ya wargaza shirin Obasanjo na neman wa’adi na uku —VON
- Shugaban La Liga ba ya kaunar Barcelona —Laporta
“Bisa damuwa da halin da marasa lafiya da iyalansu ke shiga wajen biyan kudi a asibiti, sakatare ya umarci dukkanin shugabannin asibitocin Abuja su samar da POS.
Tafida ya ce wannan matsala ba a iya Abujan ta tsaya ba, a dukkanin kasa ne wadda ta kusa zama tarihi.