Asiri na dada tonuwa
Babu wanda ya yi mamakin cewa wani katon jirgin kasar Amurka dauke da wasu manyan sundukai cike da makamai ya sauka a filin Jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano ba tare da iznin hukumomin kasar nan ba, amma sai dai kowa na mamakin yadda jirgin ya tashi, ya tafi abinsa, ba tare da […]
Babu wanda ya yi mamakin cewa wani katon jirgin kasar Amurka dauke da wasu manyan sundukai cike da makamai ya sauka a filin Jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano ba tare da iznin hukumomin kasar nan ba, amma sai dai kowa na mamakin yadda jirgin ya tashi, ya tafi abinsa, ba tare da an kammala binciken muggan makamai har da jiragen sama masu saukar angulu guda biyu wadanda aka yi wa fenti da launukan tutar Najeria da jirgin ke dauke da su ba. Wannan al’amari ya tayar da hankalin daukacin al’ummomin kasar nan ganin cewa ba wannan ne karon na farko ba da jirgi irin haka ya taba sauka a tsakiyar Arewacin Najeriya dauke da miyagun kayayyaki, musamman ma saboda ganin tsananin halin rashin tsaron da ake fama da shi a nahiyar, da kuma zaman fargabar hare-hare daga mutanen da ba a san ko su wane ne ba, wadanda suka hana yankin Arewa sakat da kashe-kashen rayuka da barnata dukiyoyin jama’a.
An san yadda kasashen da ke da alaka da kasar Faransa, wadanda kuma suka yi wa yankin Arewa-maso-Gabashin kasar nan kawanya suke haddasa fitintinun da ke hana Najeriya zaman lafiya, musamman ma kasar Chadi da ta Kamaru, wadanda uwargijiyarsu, Faransa ke bi ta kansu don kai wa ga biyan bukatunta na samun gindin zama a wannan nahiyar, saboda da kawai ta samu sukunin tatse dimbin arzikin man fetur da iskar gas da Allah Ya huwace wa yankin gabar Chadi. Jama’a da yawa na zargin kasar Chadi da boye ‘yan matan makarantar Chibok sama da 200 da aka sace, sa’annan kuma an ce tsohon Gwamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sharif wanda aka ce yana da hannu cikin kafuwar Boko Haram din asali, wacce daga bisani aka gurgunta ta, aka kuma daidaita shugabanninta don a samu sukunin ci gaba da amfani da sunan kungiyar don biyan bukatar wadanda ke amfani da Modu Sheriff don tayar da yamutsi a kasar nan.
An ga yadda shi da Shugaban kasar Chadi ke dasawa da kuma irin yadda dangantakarsu ta shafi Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya sha wanke kafafunsa yana kai ma Shugaban kasar Chadi, Idrees Debby ziyarar da ba wanda zai ce ga salsalarta ko sakamakonta.
Amma dai ana kyautata zaton cewa ko ma dai mene ne ke kai Shugaba Jonathan zuwa waccan kasa ba alheri ne ba ga Najeriya, domin kuwa an ce banza ba ta kai zomo kasuwa sai da dalili. Idan don karfafa dankon zumunta ne, me ke hana ya kai irin wannan ziyarar, wacce yake kai kasar Chadi akai-akai, zuwa Kamaru da Nijar, duk kuwa da cewa su ma uwargidansu, Faransa na amfani da su don dagula harkokin Najeriya? Kurar kasar Faransa dai ta yi kaurin suna a nahiyar tsakiyar Afrika, wacce ta kunshi kasashen Sudan da Chadi da Kamaru da Tsakiyar Afirka da Gabon da Kwango-kwango da kuma Rwanda da Burundi. Tun can fil-azal mun ga yadda ta hana kasar Kwango zaman lafiya, haka ma Gabon, mun kuma ga irin masifar kabilancin da ta haddasa a kasashen Rwanda da Burundi, inda kabilun Hutu da Tutsi suka yi wa juna katulan-makatulan, har ta kai a cikin mako guda sai da aka karkashe mutane sama da miliyan guda da rabi a dambarwar ramuwar gayya a kasashen biyu.
Baicin haka nan kuma mun fahimci yadda a ‘yan watannin baya kasar Faransa ta haddasa rikici a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (Central Africa Republic), ta kuma tura sojojinta wai don su kwantar da tarzoma, amma a zahiri taimakawa suka yi wajen ba wata kungiyar da ke kyamar Musulunci, wacce ake kira Antibalaka, damar kashe mabiyansa. Haka nan aka bi aka fatattaka Musulmi a waccan kasa, aka daidaita su, har wasu suka yi gudun hijira zuwa kasashen makwabta, kuma babu abin da kasar Faransar ta yi don hana afkuwar kisan kiyashin da aka yi wa Musulmi.
A yanzu haka ma a kasar Kamaru Musulmi ba su da katabus, domin an bi an kakkabe su daga bisa manyan mukaman gwamnati, an kuma bi an tottoshe masu hanyar habaka harkokin kasuwancinsu da na neman abincinsu. To ba ma sai an fada ba an san irin yadda wadancan manufofin nuna matsananciyar kiyayya ga Musulmi, wadanda ke afkuwa a makwantan Najeriya ke yin tasiri a wannan kasa.
Ashe kuwa kowa zai nuna damuwa saboda jin cewa shi waccan jirgin kasar Rasha, da aka kama a Kano, makare da muggan makamai, daga kasar Central Afrika ya taso, inda aka gama da dukkan Musulmin da ke kasar, aka kuma bi aka kankare wuraren ibadarsu daga doron kasa. Kayayyakin da yake dauke da su na kasar Faransa ne wacce ta yi amfani da su don biyan kazamar bukatarta a kasar.
To tunda an ce wancan jirgin Ndjamena, babban kasar Chadi, ya nufa daga Bangui, hedkwatar kasar Central Afrika, kuma tsakanin kasashen biyu baki da hanci ne, me ya kai shi yin ratse, har ya yi saukar gaggawa a birnin Kano? Kuma ko da aka ce makaman kasar Chadi ne za a kai su, me ya sa aka samu wasu bangarorin jiragen sama masu saukar ungulu da fenti irin na launin Najeria? A kasar Chadi za a yi amfani da su ko kuwa karkata su za a yi don karkashe bayin Allah a Najeriya?
Amsoshin wadannan tambayoyi ba za su yi wuyar samuwa ba sakamakon yadda al’amurra ke gudana a kasar nan dangane da sakacin gwamnati na daukar matakan da suka dace don kawo karshen wannan mummunar bala’in da ya ki ci, ya kuma ki cinyewa, Babu shakka zargin da jama’a ke yi za su tabbata game da hannun gwamnatin Najeriya cikin wannan gada-gadar da kuma hakikancewar da suke yi cewa da sanin shugabanninta ne ake haddasa masifun da ke neman gurgunta yankin Arewa, domin kuwa ba a san makomar wadancan makaman da ke dankare a cikin jirgin da aka kyale ya tashi abinsa ba. Ko da ba a samu damar sauke su a Kano ba, ana iya karkata su zuwa daya daga cikin makwabtan Najeriya, a sauke su a can, a kuma shigo da su cikin kasar nan don aikata ta’asar da aka tsara yi da su tun can farko. To jama’ar Arewacin Najeriya asiri fa na dada tonuwa, sai a yi hattara.