Asirin budurwa ya tonu bayan saurayi ya yi garkuwa da ita

An kama wata budurwa bisa zargin hada baki da saurayinta ya yi  garkuwa da ita tare da neman danginta su biya sahibin nata kudin fansa Naira miliyan 30. ’Yan Sandan sun kuma damke wata budurwar da suka hada baki saurayin wanda ake nema ya yi amfani da wayarta ya kira dangin ta farkon don neman […]

Asirin budurwa ya tonu bayan saurayi ya yi garkuwa da ita

Ankwa

An kama wata budurwa bisa zargin hada baki da saurayinta ya yi  garkuwa da ita tare da neman danginta su biya sahibin nata kudin fansa Naira miliyan 30.

’Yan Sandan sun kuma damke wata budurwar da suka hada baki saurayin wanda ake nema ya yi amfani da wayarta ya kira dangin ta farkon don neman kudin fansa.

Da yake gabatar da ’yan matan, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya ce saurayin da ake neman shi ne babban wanda ake zargi saboda shi ya kitsa garkuwar ta bogi.

Odumosu ya ce: “Akwai hadin baki a cikin yin garkuwar, saurayin ne babban wanda ake zargi kuma shi ne kashin aikata laifin.

“Za mu kamo shi mu bincike shi kan zargin hadin baki da daya daga cikin ’yan matan biyu da ta yi karyar an yi garkuwa da ita.

“Saboda tsabar wayo sai ya yi amfani da wayar ta biyun ya kira dangin ta farkon cewa an sace ’yarsu ya bukaci su biya miliyan N30 kafin ya sake ta.

“Hakan ce ta sa ’yan sanda suka shiga cikin batun aka daidaita da shi a kan za a bayar da N700,000.

“Yayin da ake kokarin kai kudin inda suka ayyana a ajiye, mun dauki matakai da suka kai ga cafke ’yan matan biyu”, inji shi.

‘Wasa nake masa’

Da take magana da ’yan jarida, wadda aka yi garkuwar karyar da ita ta ce wasa ta yi wa saurayin nata, kuma ta yi mamaki yadda ya dauki maganar da gaske sosai.

“A cikin watan Oktoba muka hadu; wata rana muna hira sai nake masa wasa cewa ya yi garkuwa da ni ya boye ni sai ya karbi kudin fansa a wurin ’yar uwata.

“Ban taba zaton ya dauki abun da gaske haka ba, sai da wata rana ya fada min cewa ya je wurin wani boka a kauye kuma sun tattauna da mutanensa kan shirin da suka yi.

“Bayan ya fada min cewa ya shirya tsaf; da ya ga alamar na tsorata sai ya yi min barazanar kisa idan na gaya wa wani, shi ya sa na yi shiru saboda shi dan a kungiyar asiri ne.

Yadda aka yi garkuwar

“Ranar 27, ga watan Nuwamba ina kan hanyar komawa gida daga makaranta sai na gan shi tare da wata budurwa a daidai 2nd Rainbow, daga nan muka tafi wani otel.

“Sai ya kira ’yar uwata yana neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansata.

“Da na ji cewa kakata ta yanke jiki ta fadi a kauye saboda abun da ta ji ya same ni, sai na ce masa kawai ya karbi ko nawa suka ba shi ya hakura.

“Ranar Alhamis ya je ya karbo kudin ya dawo otel ranar Juma’a da safe, yake fada min cewa ya karbo N600,000 sai ya sake ni saboda ya karba.

“Da na koma wurin dangina sai na ce musu wasu matasa ne suka yi garkuwa da ni na kuma yi wa ’yan sanda karya saboda barazanar da ya yi min cewa zai kashe ni tare da yaran ’yar uwata”, inji ta.

Ta ci gaba da cewa: “Bayan da na ga jakata da kuma budurwar tasa ce na fallasa duk abin da ya faru”.

Kashin kaza za a goga min’

Daya budurwar kuma ta musanta cewa tana sane kuma da hadin bakinta aka yi amfani da wayarta wurin karbar kudin fansar.

Ta ce: “Ya dai tambaye ni aron waya cewa yana son yin amfani da ita ya yi wata waya ta kasuwanci.

“Ni ban taba sanin cewa so yake ya yi amfani da waya ba wurin aikata irin wannan abun. Ina wurin aikina ne ’yan sanda suka zo kama ni”.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou