Asirin mai damfara da sunan Tata ya tonu a Katsina
A ranar Talatar nan ne dubun wata da ake zargi da yin damfara mai suna Hadiza Sani Kambarawa ta cika a yayin da wadda ta damfarar ta rutsa da ita a masallacin Juma’a na GRA, Gidan Dawa, Katsina a wajen da ake bayar da kayan tallafi na Alhaji Abdullahi Umar Tsauri wanda aka fi sani […]



A ranar Talatar nan ne dubun wata da ake zargi da yin damfara mai suna Hadiza Sani Kambarawa ta cika a yayin da wadda ta damfarar ta rutsa da ita a masallacin Juma’a na GRA, Gidan Dawa, Katsina a wajen da ake bayar da kayan tallafi na Alhaji Abdullahi Umar Tsauri wanda aka fi sani da Tata.
Wadda aka dambarar mai suna Amina Abdullaji Modoji mai sayar da katakai ta shaida wa wakilinmu cewa,”Kimanin wata shida da suka wuce, wata kawata mai suna Murja ta zo mini da labarin cewa Tata zai raba kayan alheri, suka zo da wannan mata wadda ni ban santa ba. Lokacin da suka same ni a gida ta nemi da in ba da hotuna 2 da za a kai yadda kowannenmu zai samu karuwa. To bayan mako da karbar hotunan sai Hadiza ta dawo ta ce, ke mamata ko’odineta ya ce, Tata zai fara rarraba kaya, mai Naira dubu 50 zai ba shi ’yar kurkura, mai Naira dubu 100 zai ba shi mota, domin haka don Allah in kina da Naira dubu 50 ki ba ni, in aka yi rabon na samu sai in ba ki.”
Amina ta ce, a duk lokacin da ta yi wa Hadiza magana sai ta ce kudi suna can wajen ko’odineta kuma in ta matsa za a cire hotonta ba za a ba ta komai ba. Ta ce Hadiza ta ce, ko kara aka kai ta ba wani abu ba ne. “Yau kwanana uku wurin nan ina wahala har na gane cewa yaudara da damfarata ta yi. Kuma duk abin da na fadi gata nan tsaye tana jina, don haka kudina za ta ba ni,” inji ta.
Da Aminiya ta nemi jin ta bakin Murja wadda ta sanadiyar ce Hadiza da Amina suka san juna sai ta ce,”Alakata da Hadiza ita ce zaman gidan haya, ita kuma Amina kawata ce sama da shekara goma. Hadiza ta zo mini da labarin cewa Tata zai rarraba kaya, an dauke ta a matsayin shugaba a nan yankinmu na Shinkafi, za ta amshi hotunanmu domin ta kai mu samu wannan kaya. To shi ne na gaya wa Amina wannan abin alherin. Baya ga karbar hotuna ban sake sanin komai ba, domin ba ni garin. Ga Hadiza da Amina su fadi in na san wani abu dangane da batun kudi.”
Lawal Abdulmalik wanda da ne ga Amina kuma hannunsa aka amshi kudin ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin. Lawal ya ce, tun farko zuciyarsa ta ba shi cewa akwai wani abu, to amma babu yadda zai yi saboda tuni kudin sun fita.
Da Aminiya ta juya ga Hadiza ta ce,”Na karbi wadannan kudi wajen Amina kan in na ci kurkura zan biya ta. Kuma na amshe su ne saboda yarona bai da lafiya.”
Da Aminiya ta tambaye ta cewa tun farko ta nuna mata rance take so, sai ta ci kurkurar? Hadiza ta ce, a’a. Ita dai wannan abu kaddara ce, kuma shugabar mata Binta Kala ta sanya ta karbi hotuna.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Hajiya Binta Kala da ke cikin harabar masallacin, ta ce, hakika ita ta wakilta Hadiza Sani Kambarawa domin ta samo matan da za a ba wannan tallafi ta hanyar karbo hotunansu don cike fom.
Hajiya Kala ta ce, ta tattara duk matan da ta wakilta ta yi musu bayani cewa kada su amshi ko Naira daga hannun kowace mace domin wanda ya sanya su wato Umar Tata bai ce su amshi kudi ba.
Hajiya Binta ta nesanta kanta daga wannan al’amari kuma ta ce,”Na yi bakin ciki a lokacin da na ji wannan labari. Na kira Hadiza na nuna mata rashin jin dadina a kan abin da ta aikata,”
Baya ga batun karbar Naira dubu 50 da Hadiza ta yi a hannun Amina, wasu mata da suka nemi a sakaya sunayensu su koka cewa, Hadiza ta karbi kudIn da suka fara daga Naira dubu 3 zuwa 5 da nufin za ta nemo musu rance a banki, amma ba su kara sanyata a ido ba sai a nan.
’Yan kungiyar agaji da ke wajen ne suka kwashe su zuwa wani ofishi inda a karshe Aminiya ta samu labarin an mika su ga ’yan sanda don ci gaba da bincike.