Asirin mai sayar da jabun kudi ya tonu a Hadeja

Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wani mutum da kudaden jabu, wadanda suka hada da Dalar Amurka da Sefa da kuma kudin Najeriya a garin Hadeja.An kama mutumin ne a yayin da yake kokarin cutar ’yan kasuwa da ke yin hada-hadar kudi a garin. Kamar yadda wakilinmu ya kalato, tun da farko wasu […]

Asirin mai sayar da jabun kudi ya tonu a Hadeja
Asirin mai sayar da jabun kudi ya tonu a Hadeja

Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wani mutum da kudaden jabu, wadanda suka hada da Dalar Amurka da Sefa da kuma kudin Najeriya a garin Hadeja.
An kama mutumin ne a yayin da yake kokarin cutar ’yan kasuwa da ke yin hada-hadar kudi a garin. Kamar yadda wakilinmu ya kalato, tun da farko wasu mutane ya damfara Naira dubu 70, shi ne suka tona masa asiri a lokacin da ya yi kokarin dawowa karo na biyu, domin ya sake sayar masu da kudaden na jabu.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Jigawa, Usman Tilli Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin da aka kama, an bayar da shi beli amma suna rike da motarsa har sai an kammala bincike a kansa.
Kwamishinan ya ce lallai ne za su tsaurara bincike kuma za su tabbatar doka ta yi aikinta ga wanda aka samu da laifi, domin a koya wa wadanda suke da halaye irin nasa darasi.