Asirin sabon kundin tsarin mulki ya tonu
Yanzu ’yan kwsanaki kadan suka rage kafin babban taron kasa ya wanye, kowa ya kama gabansa, kuma a daidai wannan lokacin ne ake tattafka muhawara kan muhimman abubuwan da kwamitocin taron suka tsara don mahalarta taron su amince, a samu matsayar da za a dogara da ita da sunan taron. Hakan kuwa kan sanya kungiyoyin […]
Yanzu ’yan kwsanaki kadan suka rage kafin babban taron kasa ya wanye, kowa ya kama gabansa, kuma a daidai wannan lokacin ne ake tattafka muhawara kan muhimman abubuwan da kwamitocin taron suka tsara don mahalarta taron su amince, a samu matsayar da za a dogara da ita da sunan taron. Hakan kuwa kan sanya kungiyoyin wakilai daga sassan kasar nan daban-daban su yi ta daddaga hakarkari, ana ta hayagaga, domin kowa na son a ce an amince da ra’ayinsa. Wasu nasu ra’ayoyin na son kai ne da biye zuciya, wasu kuwa suna so ne su muzanta abokan zamansu da kokarin dakile dukkan yunkurin da za su yi don kyautata halayyar zamantakewarsu da inganta abin da suka yi imani da shi.
Dangane da haka ne ake shiga, ana fita, don kulle-kullen makircin da zai bayar da damar a yi galaba, da kuma tunanin dabarun da za a bi don kange wasu daga cimma burinsu. A yanzu haka irin abin da ke faruwa ke nan game da taron kasar, domin kuwa tun ana rade-radin cewa an rigaya an samar da wani kundin tsarin mulki, sabo fil, a asirce sai ga shi Mataimakin Shugaban Babban taron, Farfesa Bolaji Akinyemi ya fito fili, firi-falo, ya fayyace haka. Wannan asirtaccen sabon kundin ya kunshi wasu batutuwa ne da rahoton taron karshen zai kunsa, cikin wani kundi mai shafukka dari da biyu, wanda aka yi wa lakabi da yarjejeniyar da shiyyoyi shida na kasar nan suka cimma a babban taron kasa da aka yi na shekarar 2014.
Shi dai wannan kundin da ya rigaya ya shiga hannun wasu manema labarai ya kunshi wasu kudurori ne da aka ce wai su ne aka cimma bayan mahawarorin da aka tafka yayin gudanar da taron wadanda suka dace da bukatun jihohin shiyyar Kudu-Kudu masu arzikin man fetur, tun kafin a kai ga tsara cikakken bayanan da rahoton babban taron zai kunsa. Kamar yadda ake zunde, wai ana can ana kokarin sayen wakilan taron daga wasu sassan kasar nan don su amince da kudurorin da aka ce an cimma yarjejeniya a kansu, wadanda kuma aka cusa cikin rahoton bogen, kuma idan har suka yi haka za a yi masu sakayya da makudan kudade, ko kuma a kirkiro masu jihohin da suke bukata.
Muhimmai daga cikin kudurorin da aka ce wai an cimma yarjejeniya a kai su ne: kebe wa jihohin da ke da arzikin man fetur kashi hamsin cikin dari, ko kuma rabin dukkan arzikin man da ke kasar nan; kirkiro sabbin jihohi goma sha uku a dukkan shiyyoyi shida na kasar nan; tsarin karba-karba a mukamin shugaban kasa tsakanin yankin Arewaci da kudancin kasar nan da kuma yin haka a mukamin gwamnan jiha tsakanin mazabun ‘yan majalisar dattijai; wa’adin shekaru shida, kuma ba kari ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi; raba arzikin kasa tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi, amma ban da kananan hukumomi, abin da ya kai wasu ga cewa an soke kananan hukumomi ke nan daga cikin matakai uku na mulkin kasar nan. Wakilan Arewaci da ke halartar taron sun tabbatar da cewa har yanzu ba a kai ga tattauna rahoton kwamitocin da ya kamata su tattauna wadancan batutuwan ba.
To amma sai dai wakilan yankin Arewacin kasar nan sun nuna tsananin adawarsu da wancan kudin da aka samar a asirce, har ma suka yi barazanar kauracewa idan aka ce za a gabatar da shi gaban taron, sun kuma musanta cewa babban taron kasar ya amince da batun soke kananan hukumomi, suka ce iyaka saninsu da abin da ya faru game da haka shi ne tabbatar da matakan kundin tsarin mulki da zai iya ba gwamnonin jihohi ikon kirkiro sabbin kananan hukumomi. Wannan na nufin cewa gwamnatocin jihohi na iya kirkiro wata sabuwar karamar hukuma, ko kuma a cire ta ba tare da yin gyara ga kundin tsarin mulki ba kafin a yi haka. Shi ma da yake tsokaci game da matsayin kananan hukumomi cikin ka’idojin yarjejeniyar da aka ce wai an cimma, Farfesa Jerry Gana, daya daga cikin jiga-jigan da suka shirya wanan taron cewa ya yi ba a soke kananan hukomi ba, “domin ana so a mayar da fallen mulkin kasar nan guda biyu ne, kuma abin lura a nan shi ne gwamnatocin tarayya da na jihohi ne kadai za su rika karbar kason dukiya daga asusun gwamnatin tarayya.”
Ana ganin cewa fitar da kananan hukumomi daga rabon dukiyar kasa, a lokacin da jama’a ke kururuwa sakamakon karancin kudaden yi masu ayyuka a yankunan karkara, zai jefa wasu sassan kasar nan cikin gagarumar wahala, ganin cewa sun dogara ne bisa dukiyar kasa da ake rarrabawa da su, kuma har yanzu ba su fara cin gajiyar dimbin arzikin da ke jijjibge a karkashin yankunansu ba. Yanzu dai asiri ya tonu game da wancan kundin da aka ce an samar da shi a asirce wanda ya kunshi kudurorin da ba za su amfani sauran jama’ar kasar nan ba sai dai ’yan shiyyar Kudu-Kudu kadai. Da ma can an tsiri irin wannan taron ne don aiwatar da wadancan kudurorin da ke cikin yarjejeniyar da aka ce an kulla su da tsakar dare domin cutar da al’ummomin Najeriya. To sai a yi hattara.