Askarawan Tsaro: Wasiƙa zuwa ga Gwamnan Zamfara
Ina roƙon Allah Ya ba ka ikon kamanta gaskiya, kuma Ya ba mu dawwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Assalamu laikum Warahamatullah Ta’ala Wabarakatu. Bayan gaisuwa da fatan alheri zuwa gare ka, da gwamnatin ka da al’ummar Jihar Zamfara baki daya.
Ina amfani da wannan dama in jinjina maka a kan irin ayyukkan ci gaba da ka ɗauko a wannan jiha tamu.
- Mali da Burkina Faso sun mika wa ECOWAS wasikar ficewarsu
- Mali da Burkina Faso sun mika wa ECOWAS wasikar ficewarsu
Kazalika, ina mai jinjina maka a kan wannan kungiya ta Askarawa da ka gabatar, ina roƙon Allah mai girma da buwaya Ya sanya mata albarka, Ya ba ma’aikatanta kwarin gwiwar ci gaba da kariya Ya tona asirin bara-gurbin da ke cikinta.
Mai girma Gwamna, na san akwai ayyuka masu tarin yawa a gaban ka don haka ba zan ɗauki lokacin ka da yawa ba.
Zan yi dan tsokaci ne a game dambarwar da na ga ana fama da ita a Karamar Hukumar Tsafe a kan rasuwar wani bawan Allah mai suna Magaji Lawali.
Mai Girma Gwamna a matsayina na wanda ba dan garin ‘Yandoto ba, amma dan Jihar Zamfara, akwai wasu muhimman abubuwa da na yi la’akari da su kuma wanda nake so in jawo hankalin ka zuwa gare su kamar haka;
1) Shugaban Askarawa da an ka naɗa na Jihar Zamfara dan garin ‘Yandoto ne.
2) An kuma tabbatar cewa, Mataimakin Shugaban Askarawar na Tsafe shi ma dan garin ‘Yandoto ne.
3) Shi wanda ya rasa ranshi wato Magaji Lawali dan garin ’Yandoto ne.
4) Ana zargin cewa an tilasta wa marigayin amsa wasu tambayoyi da kuma fadar sunayen wasu mutane a cikin faifan bidiyo wanda a yanzu haka yana hannun shugaban Askarawan na jihar (kamar yadda ake zargin tilasta ma wasu iyalan mamacin amsa cewa mahaifinsu na da alaka da ‘yan fashin daji) wanda wajen tilasta wa mamacin ne ake zargin an masa bugun kawo wuka har ya rasa rayuwarsa.
5) Akwai zargi mai karfi da ake yawo da shi cewa akwai rikicin siyasa tsakanin shugaban Askarawa na Zamfara da wasu mutane masu yawa a cikin kananan hukumomin Gusau da Tsafe musamman a cikin garin nasu na ‘Yandoto.
Bisa wadannan dalilai ne nake ganin ya kamata gwamnati ta yi nazari ta yi bincike mai zurfi ta gano gaskiyar wannan al’amari domin kauce wa matsalar da za ta iya lalata aikin wannan kungiya mai matukar muhimmanci.
Zai iya yiwu akwai wata azazza tsakanin mutanen garin na ‘Yandoto da shi shugaban Askarawa wanda cikakken bincike ne kawai zai fito da gaskiya.
Ya kamata gwamnati ta yi bincike ta gano wane ne wanda ya yi wa dan mamacin (watau Nura Magaji) tambayoyi a wani bidiyo da yake yawo a yanar gizo kuma mene ne dalilin shi na yin haka?
A yaushe ne aka gudanar da wadannan tambayoyi, kuma a wane wuri ne?
Shin kafin rasuwar mahaifin nasa ne ko bayan rasuwar mahaifin nasa?
Shin ko da ana tuhumar Magaji Lawali da aikata wadannan laifufukan, ya dace a kashe shi?
Mai girma Gwamna, a matsayinka na shugaba mai buƙatar kawo zaman lafiya, ya kamata ka yi wa kowa adalci, ka kafa kwamiti na sahihan mutane su gudanar da binchike a gano gaskiyar wannan al’amari, domin ta haka ne kawai Allah zai ba da nasarar wannan yunkuri na fada da ’yan ta’adda.
Ina roƙon Allah Ya ba ka ikon kamanta gaskiya ko yaushe, kuma Ya ba mu dawwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Allahumma Amin.
Suhailu Mohd hira da kwaddi Tudun Wada Gusau