Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata da fatan Allah Ya sa wannan
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga bayani kan hanyoyin kauce wa faruwar husuma tsakanin ma’aurata da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1. Abu na farko da zai taimaka wa ma’aurata wajen kauce wa faruwar husuma a cikin rayuwar aurensu shi ne yawan dabbaka addu’a da neman tsari ga Ubangijin Sammai da kassai Allah Madaukakin Sarki da Ya tsare aurensu daga dukkan wani abu da zai zama barazana ga zaman lafiyarsu; duk wata husuma da za ta faru Allah Ya sa ta zama dalilin karuwar alheri a cikin aurensu ba illa ba.
2. Abu na biyu da ma’aurata za su yi don kauce wa husuma shi ne kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana a koyaushe game da faruwar husuma a cikin dangantakar aurensu; kamar yadda Hauswa suke cewa, zo mu zauna zo mu saba. Duk lokacin da mutum biyu ko sama da haka suke cudanya da juna, to dole wata ran sai an samu sabawa a tsakaninsu. Akasarin lokuta husuma tana lallabowa a hankali ba zato ba tsammani sai ta bayyana cikin dangantakar ma’aurata; illar da za ta haifar kadan ne in ya kasance ma’aurata suna cikin shiri game da ita, ko ko ta haifar da akasin haka, wato husumar ta zama dalilin gyara wani nakasu da yake cikin dangantakar ma’aurata. Amma in ya kasance ma’aurata sun saki jikinsu, ba su zama cikin shiri game da husuma; to duk lokacin da ta bayyana takan yi gagarumin illa ga dangantakar ma’aurata, sannan ta bar baya da kura bayan wucewarta. Don haka koyaushe ma’aurata su zama cikin shiri game da husuma don kare kansu da aurensu daga afkawa cikin rudaninta.
3. Abu na uku da zai taimaka wa ma’aurata wajen kauce wa husuma shi ne danne fushi; bayyanar da fushi ko yaya ne yakan haifar da husuma, wata sa’ar abin da bai kai ya kawo ba sai ya zama sanadiyyar gagarumar husuma tsakanin ma’aurata saboda kasawar daya ko duka daga cikin ma’aurata ga iya danne fushinsa; domin duk maganar da mutum zai fada cikin fushi ba za ta zamo mai kyau ko mai dadi ba; za ta fito da zafi ne da niyyar rama laifin da ya haifar da wannan fushin koda kuwa a kan kuskure laifin ya faru. Sannan fushi yana rufe hankali da kyakykyawan tunani da sanin ya kamata; don haka ne Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni ga mai fushi da kada ya yi magana har sai fushin ya sauka, kuma ya nemi tsarin Allah daga Shaidan domin shi ke rura wutar fushi a cikin zuciya.
4. Hanya ta gaba da ma’aurata za su bi don kauce wa faruwar husuma, ita ce in daya ya taso daya sai ya lafa, in maigida ransa ya baci yana fada, sai uwargida ta yi shiru ta kame bakinta koda kuwa a cikin fadan nasa ya fadi wasu maganganu na munanawa gare ta, ko ya zarge ta da wani abin da ba ta yi ba ko wasu maganganu na rashin adalci gare ta, sai ta daure ta yi shiru domin in ta tanka a wannan lokaci abin rincabewa kawai zai yi; in bayan ya huce ya sauka daga fushinsa sannan sai ta kara ba shi hakuri game da laifin da ya sa shi fushin; sannan ta ce amma fa gaskiya ban ji dadin kaza-da-kaza da ka ce mini ba, ko zargin da ka yi mini ba haka yake ba ga yadda yake; shi kuma wannan lokaci sai ya ba ta hakuri koda yana ganin daidai ne abin da ya yi; kada ya ce zai dage ya nuna shi a kan daidai yake ko shi lallai sai ya kare kansa a kan ba daidai din da uwargida ta nuna ya yi mata. In kuma uwargida ce ranta ya baci game da wani abu da maigida ya yi, a lokacin da take cikin bayyana fushinta, sai maigida ya lafa har sa ta sauka sannan ya yi abu mafi dacewa kamar yadda bayani ya gabata a sama.
Darasi abin dauka ga ma’aurata shi ne na Imam Ahmad bn Hambal (Rahimahullah), ya fadi bayan rasuwar maidakinsa Ummu Salih cewa: “A cikin shekara talatin din da muka yi tare da ita; sabawa ta rana daya ba ta taba shiga tsakaninmu ba.” Sai aka tambaye shi ta yaya hakan ya faru? Sai ya ce: “ Duk lokacin da ranta ya baci, ta yi kokarin yin jayayya, sai in yi shiru; ita ma duk lokacin da raina ya baci na yi kokarin yin jayayya, sai ta yi shiru.” Lallai wannan wani kyakykyawan darasi ne da ya kamata duk ma’aurata su yi koyi da shi cikin rayuwar aurensu.
Sai mako na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawaSa a kodayaushe, amin.