Aston Villa ta lashe babbar gasar Turai karon farko cikin shekaru 44

Unai Emery ya shiga cikin fitattun masu horaswa da suka lashe manyan kofunan gasar Turai sau biyar.

Aston Villa ta lashe babbar gasar Turai karon farko cikin shekaru 44

Aston Villa ta lashe gasar Europa League ta bana, bayan doke Freiburg ta Jamus da ci 3-0 a yammacin wannan Larabar.

Youri Tielemans, Emeliano Buendia da Morgan Rogers ne suka ci wa Villa  ƙwallayen da suka tabbatar da wannan nasara a filin wasa na Tupras Stadyumu.

Wannan ita ce nasara a babbar gasar Turai karon farko da ƙungiyar ta samu tun bayan lashe babban kofin Turai na European Cup a 1982.

Da wannan sakamakon, Unai Emery ya shiga cikin fitattun masu horaswa da suka lashe manyan kofunan gasar Turai sau biyar bayan da Aston Villa ta yi nasara a Istanbul.

Emery yanzu shi ne koci na huɗu da ya lashe manyan kofin gasar Turai sau biyar, bayan fitattun masu horaswa kamar Giovanni Trapattoni da Carlo Ancelotti, da kuma tsohon kocin Chelsea da Manchester United, José Mourinho.