Asusun ajiyar waje na Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 2.2

A cikin kasa da kwana 30 asusun ajiyar waje na Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 2.2, inda zuwa ranar 19 ga Maris ya zama saura Dala biliyan 32.30 Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada gibin da aka samu a asusun ya kai kashi 6.9 cikin 100 a tsakanin wadannan kwanakin.A bara asusun ajiyar ya […]

Asusun ajiyar waje na Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 2.2
Asusun ajiyar waje na Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 2.2

A cikin kasa da kwana 30 asusun ajiyar waje na Najeriya ya samu gibin Dala biliyan 2.2, inda zuwa ranar 19 ga Maris ya zama saura Dala biliyan 32.30

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada gibin da aka samu a asusun ya kai kashi 6.9 cikin 100 a tsakanin wadannan kwanakin.
A bara asusun ajiyar ya samu gibin Dala biliyan 8.14 wanda ya sanya gibin ya kasance kashi 21 cikin 100.
A kwanakin nan CBN ya dauki wadansu matakan magance gibin da ake samu a asusun ajiyar waje na Najeriya. A cikin matakan da bankin ya dauka akwai dakatar da biyan kudin kayayyakin da ake shigowa da su ta hanyar amfani da Dala.
Ci gaba da tsakurar asusun ne ya sanya bankin ya dakatar da shirin cinikayyar canjin kudi na RDAS da WDAS, shirin da masu shigo da kayayyaki suke karbar Dala daga Babban Bankin Najeriya.
Wani masanin harkar tsimi da tanadi kuma babban jami’in gudanarwar na kamfanin APT Securities and Funds Limited, Mista Kasimu Garba Kurfi ya bayyana gibin da ake samu a asusun ajiyar waje ba abin mamaki ba ne, domin hanyoyin da suke samar da kudaden shiga a kasar nan sun ragu.
“A lokacin da gangar danyen mai take Dala 50 a kan kowace ganga, hakan ya bayyana an samu raguwar kashi 45 na kudin shigar da ake samu daga bangaren mai. A bangaren kasuwannin hannu jari kuwa, masu zuba jari sun daina zuba jari, sun kuma kwashe ribar da suka samu daga kasuwannin, inda suka canja Naira zuwa sauran kudaden kasashen daban-daban, sannan kasuwar hannun jari ta kasashen waje a Najeriya ba ta tafiya yarda ta kamata saboda karatowar zabe.” Inji Kurfi.
A dangane da bangaren yadda ake bukatar Dala kuma, sai Kurfi ya bayyana cewa ’yan siyasa ma sun kara haifar da matsalar, inda suka fi amfani da kudaden kasashen waje maimakon kudin gida.
“Fiye da gwamnoni 19 ba za su koma mukaminsu ba, don haka sun tashi haikan wajen canja kudinsu daga Naira zuwa kudaden kasashen waje, don su fitar da su daga Najeriya.” Inji shi.
A lokacin da Aminiya ta tuntubi Daraktan Babban Bankin Najeriya a bangaren sadarwa, Ibrahim Mu’azu kan dalilin da ya sa ake samun raguwa a asusun ajiyar waje na Najeriya, sai ya bayyana hakan ya samu nasaba ne dalilin yawaitar bukatar Dala ne da kuma karancinta a kasuwa.
Ibrahim ya ce ana bukatar Dala ne wajen shigo da mai daga kasashen waje, ko ababen hawa, ko cire kudaden daga asusun ajiyar waje don tafiyar da ilimi da lafiya da sauransu.