Asusun ajiyar waje ya ragu da Dala biliyan 2.8 a kasa da wata biyu
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana asusun ajiyar waje na Najeriya ya ragu da Dala biliyan 2.8 kasa da wata biyu. A ranar 19 ga Disamba, 2014 akwai kimanin Dala biliyan 35.13 a cikin asusun, inda a ranar Alhamis 19 ga Fabrairu, 2014 ya zama saura Dala biliyan 32.30.An bayyana dalilai da dama ne suka […]

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana asusun ajiyar waje na Najeriya ya ragu da Dala biliyan 2.8 kasa da wata biyu.
A ranar 19 ga Disamba, 2014 akwai kimanin Dala biliyan 35.13 a cikin asusun, inda a ranar Alhamis 19 ga Fabrairu, 2014 ya zama saura Dala biliyan 32.30.
An bayyana dalilai da dama ne suka sanya asusun ajiyar ya ragu, ciki har da faduwar farashin mai da kuma faduwar darajar Naira a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.
CBN ya tabbatar cewa ya yi amfani da kudin asusun ajiyar wajen ne don kare Naira tun da darajarta ta fara faduwa a Nuwamban bara.
CBN ya dakatar da hada-hadar kasuwancinsa na shirin rDAS da wDAS sakamakon faduwar farashin mai da kuma raguwar asusun ajiyar waje.
“A ’yan kwanakin nan bayan farashin mai ya fadi warwas, inda aka samu raguwar kudin shiga, hakan ya sanya bankinmu ya samu babban gibi a shirin rDAS, wanda hakan ba haifar mana da da mai ido ba.
“Hakan ya sanya aka rika tsakurar kudi daga asusun ajiya na waje, inda duk da hakan kwalliya ba ta biya kudin sabulu a wurin jama’a da ma kansa tattalin arzikin kasar nan.” Inji CBN.
Asusun ajiya na waje ya ragu da kashi 20 cikin 100 daga Dala biliyan 42.85 a shekarar 2013 zuwa Dala biliyan 34.24 a ranar 31 ga Disamba, 2014.
Najeriya ta ta’allaka a kan kudin da ta sayar man kasar a kasuwannin duniya ne wajen samun kudin shiga.
Amfanin asusun ajiya na kasashen waje ya hada da taimaka wa kudin cikin gida da amfani da shi wajen hada-hada ko cinikayya da kasashen waje da kuma kawo dauki idan wani abu ya samu kudin cikin gida.