Asusun BSF ya raba kayayyakin noma ga ’yan gudun hijirar da suka dawo gida a Yobe

A kokarinta na dawo da walwalar rayuwa ga ’yan gudun hijirar da suka koma gida, Asusun Tallafa wa Wadanda Rikici ya shafa wacce atakaice ake kira BSF da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe ta raba kayan noman rani ga fiye da iyalai dubu daya a Karamar Hukumar Yunusari. Shirin wanda ya gudana a garin Mazagum […]

Asusun BSF ya raba kayayyakin noma ga ’yan gudun hijirar da suka dawo gida a Yobe
Asusun BSF ya raba kayayyakin noma ga ’yan gudun hijirar da suka dawo gida a Yobe

A kokarinta na dawo da walwalar rayuwa ga ’yan gudun hijirar da suka koma gida, Asusun Tallafa wa Wadanda Rikici ya shafa wacce atakaice ake kira BSF da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe ta raba kayan noman rani ga fiye da iyalai dubu daya a Karamar Hukumar Yunusari.

Shirin wanda ya gudana a garin Mazagum an yi shi ne don kaddamar da shirin tallafin noman rani na wannan shekarar  a yankin Arewa maso Gabas ga wadanda suka koma gida wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Gwamna Ibrahim Gaidam wanda Kwamishinan Albarkatun Noma da Albarkatun kasa na Jihar ya wakilta, Injiniya Mustapha Gajerima ya ce “An gudanar da shirin ne a lokacin da ya dace kuma zai tallafawa kokarin da Gwamnatin Jihar take yi na dawo da walwalar rayuwa ga mutanen da rikicin ya shafa.

A jawabinsa, Shugaban Asusun BSF, Laftanar Janar T.Y Danjuma mai ritaya wanda Mai Magana da Yawun Cibiyar, Alkasim Abdulkadir ya wakilta ya ce shirin na son cimma burin rage wahalar da mutane sha wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Cibiyar na son rage radadin da ke damun mutanen da rikicin ya shafa.

“Cibiyar tana son ta sanya iyalai dubu uku cikin shirin a jihohi uku na Borno da Yobe da kuma Adamawa wadanda rikicin ya fi shafa sosai don su zama masu dogaro da kansu’’. Inji shi.

Da yake yi wa manema labarai karin haske Daraktar Shirye-shirye ta Cibiyar BSF, Nana Tanko ta bayyana cewa magidanta 200 ne daga garuruwa biyar da suka hada da Mazagum da Bultuwa da Dekwa da Degeltura da kuma Mairari suka amfana. Kayayyakin da aka raba sun hada da kananan taraktocin noma da na’urar feshi da injin tura ruwa da bututun ban ruwa da takin zamani na ruwa da maganin kwari.