Asusun ginin masallacin layin Bagobiri a Kalaba ya fara kauri

An tara kimanin Naira miliyan biyu nan take a wajen kaddamar da asusun ginin masallaci a unguwar Hausa layin Bagobiri da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba. Shugaban kwamitin tsare-tsaren kaddamar da asusun, Alhaji Ali Shitu  Zabainawa ne ya shaida wa Aminiya haka jim kadan da kammala kaddamarwar, wadda al’ummar musulmin jihar suka halarta kuma […]

Asusun ginin masallacin layin Bagobiri a Kalaba ya fara kauri

An tara kimanin Naira miliyan biyu nan take a wajen kaddamar da asusun ginin masallaci a unguwar Hausa layin Bagobiri da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba.
Shugaban kwamitin tsare-tsaren kaddamar da asusun, Alhaji Ali Shitu  Zabainawa ne ya shaida wa Aminiya haka jim kadan da kammala kaddamarwar, wadda al’ummar musulmin jihar suka halarta kuma suka bayar da gudunmawa.  Ana sa ran masallacin ya zama irin fasalin wanda ke  Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan.
Alhaji Zabainawa ya ce duk da wannan jimla da aka samu, akwai alkawuran kudi da jama’a suka yi, wanda ake sa rai da kuma fata Allah Ya ba su ikon cikawa.
Dangane da rade-radin rashin isasshen filin gina masallacin da ma’ajiyar motoci, shugaban kwamitin ya warware shakku da ake da shi.  “Eh! A nan ba mu da fili wadatacce, amma masu gidan da ke kusa da masallacin sun nuna za su sayar da gidansu, tun ma kafin wannan bukatar tamu ta taso, ba kuma tursasa su aka yi ba. Idan Allah Ya sa kudi ya wadata a hannunmu za mu tunkare su. Idan Allah Ya sa muka samu wannan wurin, muka kara da shi zai ishe mu a wadace”. Inji shi.
Game da maganar ko gwamnatin jiha ta san da zancen aikin masallacin kuma ta amince, sai Alhaji Ali Zabainawa ya ce ta yarda, “Sun sanya mana hannu a takardunmu na neman izni, har ma sun amince mu ci gaba da aiki. Hatta shi kansa ma Gwamna Liyel Imoke, mun aika masa da takardar neman taimako kuma sakataren da takardarmu ta bi ta hannunsa ya yi farin ciki, kuma ya nuna mana sha’awar irin abin da suke so ke nan”.
A karshe ya nemi ilahirin musulmi su taimaka da kayan aiki ko kudi don a samu abin da za a kammala ginin masallacin, wanda idan har aka gama shi zai kasance na biyu a duk fadin Nijeriya, sannan kuma na farko a fadin Kudu maso Gabashin kasar nan.