Asusun PTF ya kyautata rayuwar al’umma a lokacin Abacha
A watan Oktoba na shekarar 1994, marigayi Shugaba Sani Abacha da ya yi mulki Najeriya ya bayyana karin kudin man fetur. Wannan abu ya tada kura a kasar nan, wanda ya sa ‘yan kasa suka rinka korafi suna masu nuna adawar su ga karin farashi. Hakan ta sa Shugaba Abacha yin dogon tunani da nazari […]
A watan Oktoba na shekarar 1994, marigayi Shugaba Sani Abacha da ya yi mulki Najeriya ya bayyana karin kudin man fetur. Wannan abu ya tada kura a kasar nan, wanda ya sa ‘yan kasa suka rinka korafi suna masu nuna adawar su ga karin farashi.
Hakan ta sa Shugaba Abacha yin dogon tunani da nazari a kan lamarin. Na farko dai bai kara farashin man fetur ba sai bisa wasu muhimman dalilai, sannan kuma shi ba shugaba ba ne mai son uzzura wa al’ummar da yake mulka, kamar yadda ake yawan jiyo shi yana cewa “an gina gwamnati ne don al’umma, ba don a ci riba ba.” Don haka sai ya kirkiro da wani asusu, wanda zai rage wa al’umma radadin talaucin da suke ciki, zai kuma ciyar da kasar gaba. Sunan asusun shi ne ‘Petroleum Trust Fund’ (PTF), sunan shugaban asusun da ya nada shi ne Janar Muhammadu Buhari, sai wani mai suna chief Tayo Akpata a matsayin sakatare. An kuma kaddamar da su a watan Maris na shekarar 1995. Daga nan Shugaba Sani Abacha ya rinka turo musu da kudi, su kuma suna gudanar da ayyukan alheri.
Da fari dai, al’ummar Najeriya ba su gaskata gaskiyar Shugaba Abacha a kan wannan kuduri ba, amma daga bisani hakika kowa ya gani a kasa. Ga misalan aikace-aikacen da Asusun ya gunadar:-
1. Fannin lafiya ya samu babban tagomashi, domin kuwa an gina manyan asibotoci a karkashin asusun, an kuma gyara kusan kowanne babban asibiti a kasar nan.
*Sannan an sawo motocin daukar marasa lafiya (Ambulance) masu yawan gaske, tare da rarraba su izuwa asibitocin kasar nan.
*An tura da tabarau ga asibitoci don rarraba wa masu matsalar idanu kyauta.
* An sawo kayayyakin kula da masu cutar kanjamau tare da magunguna a karkashin shirin (HIb/AIDs Interbention programme), inda aka rika bayar da su kyauta ga mabukata.
* An bude ofisoshin sayar da magunguna a karkashin tsarin (PTF drug Rebolbing fund) a duk manyan asibitoci, inda ake sayarwa da jama’a magani kasa da yadda farashin sa yake a kasuwa, ko a sauran shagunan da ba na gwamnati ba. A kan haka ne ma aka taba kama wani jami’in gwamnati yana son karkatar da akalar magungunan, inda daga karshe shugaban asusun Buhari ya fusata da hakan, sannan ya kai jami’in gaban kuliya, inda aka garkame shi.
2. Gine-gine. Wannan asusu, ya yi gine-gine masu tarin yawa a kasar nan. Sannan an kawar da rashawa a tsarin kwangila, domin asusun yana kwace kwangilar sa ne ga duk wanda ya yi masa wasa. Misalin gine-ginen su ne;
*Ginin rukunin gidaje a wuse da ke Abuja (Residential estate) don saukake wa ma’aikata mallakar muhalli cikin rahusa.
*Fara Gina Matatar ruwa a Okpella.
* Gina babban titin edpress da ke tsakanin Enugu da Anacha.
* Sannan an gyara wasu manyan tituna a sassan kasar, inda aka zuba musu kwalta mai inganci tare da gina musu magudanan ruwa.
3. Ilimi. Wannan asusu ya samar da tallafi ga fannin ilimi. An gina makarantu masu yawa a cikin wannan shiri. Har yau gine-ginen dakunan karatu a jami’o’i da kwalejoji, wanda asusun PTF ya gina suna nan dauke da tambarin asusun. Al’umma shaida ne, asusun ya rarraba littattafai da abin rubutu kyauta ga dalibai.
4. Abinci. Asusun ya samar da kayyakin abinci a farashi mai rahusa,inda ake sayar wa mutane a farashi kasa da farashin kasuwa.
5. Ciyar da tattalin arzikin kasa gaba. Wannan asusu ya yi dabarar bai wa ‘yan kasa kwangilar duk wasu ayyuka da zai gabatar. Kuma yana sanya sharadin cewa dole ne dan kwangila ya sawo kayansa a nan gida Najeriya (sai dai idan abin da ake bukata ba a yinsa a gida). A kan haka aka ce kamfanonin magani irin su Emzor pharmaceuticals, da na suminti kamar Leferge da na fenti misalin IPWA ltd da wasunsu sun amfana, har suna daukar ma’aikata. Wannan abu ya taimaka wajen kara habaka tattalin arziki, tare da samar da aikin yi.
6. Samar da motocin sufuri masu zirga-zirga da jama’a a kan farashi mai rahusa a karkashin shirin (PTF subsidise commercial behicle)
A karshe, bayan rasuwar Janar Sani Abacha, Shugaba Obasanjo ya sauke Shugaba Buhari, tare da nada Mallam Haruna Adamu shugaban asusun. A wannan lokacin asusun na dauke da kudi sama da Naira biliyan dari. Shine aka ce Shugaba Buhari ya tara ma’aikatansa tare da yi musu jawabin bankwana, sannan ya ce duk wani abu da ake son bincikawa yana nan a rubuce. Daga nan ya sauko daga saman bene ya shiga motar sa ya nufi Daura.
Obasanjo ya yi bincike matuka kafin ya rufe wannan asusu, amma duk adawar sa ga Marigayi Sani Abacha bai taba fitowa fili ya zargi asusun PTF ba, hukumar EFCC kuwa ba ta taba gayyatar Shugaba Buhari don tuhumar sa da almundahana a cikin asusun ba.
Da fatan Allah ya jikan Janar Sani Abacha, Allah ya taimaki Shugaba Buhari a kan shugabancin kasa da yake yi. Amin
Sadik Tukur Gwarzo 08060869978