ASUU ba ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya ba

Wakilan kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU, ta zauna a teburin sulhu da wakilcin tsagin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin minisatan kwadago da daukar ma’aikata na Nijeriya, Dokta. Chris Ngige a yammacin laraba, akan lamuran da suka shafi yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi tsawon watanni bakwai. Kungiyar ASUU basu samu daidaito da bangaren gwamnati […]

ASUU ba ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya ba

Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi

Wakilan kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU, ta zauna a teburin sulhu da wakilcin tsagin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin minisatan kwadago da daukar ma’aikata na Nijeriya, Dokta. Chris Ngige a yammacin laraba, akan lamuran da suka shafi yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi tsawon watanni bakwai.
Kungiyar ASUU basu samu daidaito da bangaren gwamnati ba, ASUU ta ce ba za su koma bakin aiki ba har sai gwamnati ta biya musu dukkan bukatunsu.
Kungiyar ta shelanta wa dukkan ‘yan kungiyar da su ci gaba da zama a gida har sai an cimma matsaya da gwamnatin tarayya akan bukatunsu.
ASUU ta ce, za a ci gaba da zama a teburin sulhu amma yanzu za su ci gaba da yajin aiki.
Sauran bayani zai zo daga baya.