ASUU ta kulla yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya

kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya kan hobbasar gwamnatin na aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2009.Shugaban kungiyar ASUU Dokta Nasir Fagge wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar ya ce duk da cewa an yi alkawari ne shekara hudu da suka gabata ba tare da aiwatar da ita […]

ASUU ta kulla yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya
ASUU ta kulla yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya

kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya kan hobbasar gwamnatin na aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2009.
Shugaban kungiyar ASUU Dokta Nasir Fagge wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar ya ce duk da cewa an yi alkawari ne shekara hudu da suka gabata ba tare da aiwatar da ita ba, har yanzu akwai damar taimaka wa Najeriya wajen aiwatar da ita cikakkiyarta.
Sai dai ya ce, babbar majalisar gudanarwar ASUU ne za ta janye yajin aikin, inda ya ce za ta yi taro a cikin wannan mako.
Dokta Fagge ya ce duk da cewa kasashe irin su Brazil da Malesiya da suka zuba dukiya ga ilimi jami’o’insu sun bar Najeriya a baya, abu mai kyau zai iya aukuwa a Najeriya unda Gwamnain Tarayya ta yi alkawarin sauya hali wajen ba jami’o’i isassun kudi domin gudanar da bincike domin samar da ingantaccen ilimi da zai samar da kwararrun ma’aikata a ciki da wajen Najeriya.
Minista mai kula da Ma’aikatar Ilimi Farfesa Nyesom Wike ya ce, batutuwan da ASUU ta gabatar an warware su, don haka kungiyar za ta janye yajin aikin kwanan nan.
“Muna farin ciki cewa a karshe mun ga sanya hannu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, tare da shaidae Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC). Hakan na nuna an warware matsalar da ake magana.”
Shugaban kungiyar NLC na kasa, Abdulwahed Omar, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kungiyar kwadago ya ce kwanan nan ’yan Najeriya za su fara cin gajiyar yarjejeniyar da aka sanya hannu a kai.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, MacJohn Onyekwere Nwaobiala, wanda ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya ya ce, “A wurina sanya hannun ASUU na nufin an kawo karshen yajin aikin.”
Sauran wadanda suka halarci wurin sanya hannunsuna hada da Shugabannin jami’o’in Bayero da ke Kano da na Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi da na Jami’ar Ibadan da na Fatakwal da na Legas wadanda shiga tsakani da suka yi ne ya jawo aka kulla yarjejeniya a tsakanin bangarorin biyu.
A ranar Litinin ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta saki Naira biliyan 200 ga asusun inganta jami’o’i na kasar nan.
 Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata wasika da aka aika ga Babban Akantan Tarayya mai kwanan wata 10 ga Disamba, 2013 dauke da sanya hannun Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Tunde Lemo.
kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta tsunduma yajin aiki tun ranar 1 ga Yuli, kuma tattaunawa daban-daban da aka rika da jami’an Gwamnatin Tarayya ciki har da ganawar awa 13 da Shugaba Goodluck Jonathan har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba su kawo karshen yajin aikin na wata biyar ba.