AT Gwarzo ya janye wa Barau a takarar Sanatan Kano ta Arewa

Gwarzo ya sanar da janye takararsa ta kujerar Sanata domin mara wa Sanata Barau Jibrin baya

AT Gwarzo ya janye wa Barau a takarar Sanatan Kano ta Arewa

Tsohon Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya janye wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin daga takarar Sanatan Kano ta Arewa.

AT Gwarzo ya janye wa Barau ne a yayin wani zama da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi nasarar sasanta manyan jiga-jigan jam’iyyar APC biyu a Kano ta Arewa.

An ganin sasancin Barau da AT Gwarzo zai ƙara haɗin kai a jam’iyyar gabanin zaɓe mai zuwa.

Wannan kuwa na zuwa ne washegarin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jami’yyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci Gwarzo domin wata ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bayan APC ta zaɓi Barau a matsayin ɗan takarar kujerar.

Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya tabbatar da sasancin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Laraba.

Ya ce a ƙarshen taron Gwarzo ya sanar da janye takararsa ta kujerar Sanata domin mara wa Sanata Barau Jibrin baya.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, da Shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, da sauransu.

Ana kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara wajen ƙarfafa APC a yankin Sanatan Kano ta Arewa, inda rikicin cikin gida ya fara barazanar raba kan magoya bayan jam’iyyar.

Bayan janyewar tasa, Gwarzo ya bayyana biyayyarsa ga muradun jam’iyyar tare da nuna shirinsa na yin aiki tare da Barau a zaɓe mai zuwa.

Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce wannan mataki na iya ƙara wa jam’iyyar ƙarfi sosai a yankin, ganin yadda duka mutanen biyu suke da gagarumar farin jini a tsakanin talakawa.