Atiku Abubakar ya bar APC

Tsohon Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi watsi da Jam’iyyar APC mai mulki. Tsohon Shugaban Kasar ya sanar da hakan ne a wata wasika da aika wa Jaridar Premiun Times. A wasikar, Atiku ya nuna yadda ‘yan APC suka zo har gida a ranar 19 ga watan Disamba, na shekarar 2013, inda suka bukaci ya […]

Atiku Abubakar ya bar APC

Tsohon Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi watsi da Jam’iyyar APC mai mulki.

Tsohon Shugaban Kasar ya sanar da hakan ne a wata wasika da aika wa Jaridar Premiun Times.

A wasikar, Atiku ya nuna yadda ‘yan APC suka zo har gida a ranar 19 ga watan Disamba, na shekarar 2013, inda suka bukaci ya dawo jam’iyyar. Sannan ya amince ya shiga jam’iyyar bayan jam’iyyarsa ta PDP ta shiga rudu da rabowar kai a lokacin.

Hakanan kuma ya nuna yadda wani Gwamna a Jam’iyyar APC ya rubuta wasika ta musamman zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda ya nuna masa cewa fa anyi watsi da wasu manyan jigogin jam’iyyar, amma kuma a cewarsa, har yanzu babu abin da aka yi domin magance wannan batun da wannan gwamnan ya kawo.

Don haka ne sai ya yanke shawarar barin jam’iyyar bayan ya yi shawara da magoya bayansa “Bayan na yi addu’a wajen Allah, kuma na yi shawara da iyalai, magoya baya da sauran ‘yan uwa da abokanan arziki, ni Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa, na bar Jam’iyyar APC, kafin in yanke shawarar abin da zan yin an gaba.”