Atiku ba zai ci zabe ba —Edwin Clark
Edwin Clark ga Okowa ya nemi Okowa ya janye takararsa ta mataimakin Atiku
Dattijon PDP, Cif Edwin Clark ya bukaci Gwamnan Delta, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, da abokin takararsa Ifeanyi Okowa, ba za su ci zaben da ke tafe ba.
Clark wanda shi ne shugaban Gamayyar Kungiyar Neja Delta ta PANDEFF da kuma kungiyar jagororin yankin Kudu da na Middle Belt (SMBLF), ya kuma bukaci Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, ya janye takararsa ta mataimakin Atiku.
Tsohon Ministan Yada Labaran ya zargi Okowa da amfani da dukiyar yankin Neja Delta wajen yakin neman zaben Atiku, inda ya buakci gwamnan ya fito ya bai wa al’ummar Kudu hakuri, ya kuma janye takararsa.
Ya bayyana haka ne ta wasikar da PANDEFF ta aika Okowa, wadda aka karanto a taron manema labaran da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
A cewarsa, Okowa ya saba wa matsayar da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsakin yankin da suka amince da shi na kin mara wa duk wani dan siyasa da bai fito daga yankinsu baya ba, musamman ma Atiku.
“A yau na tabbatar da kafi dukkanin sojojin da suka jagoranci yankin Neja Delta mulkin kama karya tun kirkirarsa a shekarar 1991.
“Hakan ya sa na fahimci dalilin da ya sa ba kunya ka ci amanar yankinka saboda son zuciyarka.
“Da yardar Allah burinka ba zai cika ba. Watakila ka manta nauyin laifinka ga mutanen yankin Kudancin Najeriya.
“Kuma don boye munin abin da ka aikata ka sanya wani ya boye guntun kashinka ta hanyar sanya wani ya jagoranci taron gwamnoni 17 na Kudu a gidan gwamnati ranar 11 ga watan Mayun 2021.
“A taron ka mata har cewa ka yi kada wani a cikinsu da aka nemi ya karbi takarar mataimakin shugaban kasa, kuma duk muka amince? Ashe share wa kanka hanya ka yi”, in ji shi.
Clark ya kuma bukaci Okowa ya fito ya bai wa al’ummar yankin na PDP da APC hakuri, saboda wannan tabargaza da ya aikata, ya kuma janye takarar mataimakin shugaban kasar da yake yi.