Atiku bai halarci taron Majalisar Zantarwar APC ba
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar bai halarci taron shugabannin jam’iyyar APC wanda shugaba Buhari ya jagoranta. Taron wanda aka yi shi a dakin taro na fadar shugaban kasa an fara shi ne da misalin karfe takwas da rabi na safe a Abuja. Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron wanda shugaban majalisar dattawa, Bukola […]

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar bai halarci taron shugabannin jam’iyyar APC wanda shugaba Buhari ya jagoranta.
Taron wanda aka yi shi a dakin taro na fadar shugaban kasa an fara shi ne da misalin karfe takwas da rabi na safe a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron wanda shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara da jagoran majalisar dattawa Ahmad Lawan sun isa wurin bayan miniti 10 da fara taron da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban jam’iyyar na kasa, John Odigie-Oyegun suka halarta.