Atiku da Kirfi sun nemi a dauki matakin raya yankin Arewa maso Gabas
An bukaci masu rike da mukaman siyasa da kwararru da sauran masu ruwa da tsaki da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas su bullo da dabaru da hanyoyin yin amfani da albarkatu dan Adam da albarkatun kasa da ke yankin domin raya yankin.Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya yi wannan kira a […]
An bukaci masu rike da mukaman siyasa da kwararru da sauran masu ruwa da tsaki da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas su bullo da dabaru da hanyoyin yin amfani da albarkatu dan Adam da albarkatun kasa da ke yankin domin raya yankin.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya yi wannan kira a Gombe a shekaranjiya Laraba, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin taron Tattalin Arzki na Arewa maso Gabas karo na biyu da jihohi shida na yankin shirya domin tsara yadda yankin zai ci gaba.
Atiku ya nuna damuwa kan yadda aka yi ta shirya irin wadannan tarurruka ba ga yankin Arewa maso Gabas kadai ba, ga daukacin Arewa, amma a koyaushe sai a kasa cimma nasarar da ta kamata sakamakon gazawar manyan masu ruwa da tsaki na su bayar da gudunamwar da ta wajaba domin cimma nasarar bukatun da aka gabatar.
“Wajibi ne mu nuna sadaukar da kai a matsayinmu na al’umma domin mu bunkasa yankinmu, ba batu ne surutan burgewa ba, a’a a dauki matakan da suka wajaba domin bin alkiblar da ta dace. Idan muka hada kai za mu cimma nasarar abin da muke fata nan gaba, kuma mu bunkasa yankin ta hanyar yin amfani da dimbin albarkatun da ke jibge a yankin,” inji shi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya nuna jin dadinsa kan yadda gwamnonin yankin suka rungumi shawarar da dattawan yankin suka bullo da ita wadda daga farko gwamnonin suka ki yin haka.
Alhaji Bello Kirfi ya bukaci gwamnonin su sake dawo da kwalejojin horar da malamai a yankin domin horar da kwararrun malamai da za su koyar a makaranun ankin domin samar da ingantaccen ilimi ga yaran yankin.
Ya yi watsi da kididdigar da tsohon Ministan Tsare-Tsaren kasa ya bayar a ranar farko na taron inda ya dora yankin a kan yankin Arewa maso Yamma. Ya kuma ce ana tauye yankin wajen nade-naden mukaman Gwamnatin Tarayya duk da ya fi wasu yankuna yawan jama’a.