Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri
Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun.
![Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/atiku-obasanjo.jpg)
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo.
Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun.
A ranar Litinin ne Atiku tare da rakiyarsa ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya.
Isar tawagar Atiku da tawagarsa gidan Obasanjo ke da wuya shugabannin biyu suka sanya labule domin ganawar sirri.