Gobe Kotun Koli za ta bayyana ainihin wanda ya lashe zaben 2023

Kotun Koli ta sanya gobe Alhamis a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari’ar da Atiku Abubakar da Peter Obi suke kalubalantar nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2023.

Gobe Kotun Koli za ta bayyana ainihin wanda ya lashe zaben 2023

Kotun Koli ta sanya gobe Alhamis a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Peter Obi suke kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya shigar da karar ne kamar takwarana na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.

Atiku da Peter Obi kowannensu na ikirarin shi ne ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 da kuri’u mafiya rinjaye, duk da cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Tinubu ne ya yi nasara, aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Daraktan Yada Labarai na Kotun Koli, Festus Akande ya sanar a ranar Laraba cewa a ranar Alhamis alkalan kotun za hu yanke hukunci kan shari’ar zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ranar Litinin PDP da LP da ’yan takararsu suka gabatar da shaida a gaban kotun koli, wadda ta yi watsi da karar Jam’iyyar APM da dan takararta, Chichi Ojei, bayan sun janye kararsu.

Atiku, Obi da jam’iyyunsu, sun daukaka kara zuwa kotun koli ne saboda rashin gamsuwarsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na ranar 6 ga watan Satumba, wanda ya yi watsi da kararsu saboda rashin gamsassun hujjoji.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano