Atiku da Wike na shirin tarwatsa PDP
Wike yana ganin idan har aka tafi a hakan to shi fa bangarensa an gama da shi a siyasance.
Jam’iyyar PDP wacce daman take farfadowa daga cikin rikicin shugabanci na kin amincewar tsohon shugabanta Uche Secondus ya sauka daga mukaminsa, sai kuma ga wani babban rikici ya sake dabaibaye jam’iyyar, wanda ga dukkan alamu na neman kaita ruwa.
Zaben fid-da-gwani na Jam’iyyar PDP, ya sake jefa ta cikin rikici, wanda ake ganin kan iya kawo nakasu ga samun nasarar jam’iyyar a zaben da ke tafe.
- An kama matar da ta sheka wa matashi tafasasshen ruwa a Kano
- Kotu ta ba PDP umarnin sake zaben fidda dan takarar Gwamna a Zamfara
Atiku Abubakar dai shi ne dan takarar da wakilai suka zaba a ranar 22 ga watan Mayu, 2022, bayan fafatawar da yayi da sauran wasu ’yan takarar wanda daya daga cikinsu shi ne gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike.
Zaben da ya ba wa Atiku nasara ya bar baya da kura
Manyan Jam’iyyar suna ta kai gwauro sukai mari don ganin wannan matsala bata dore ba, har zuwa lokacin zabe wanda ke karatowa.
Mista Wike ya kasance dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP. Inda ya sha kaye a hannun tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.
Yayin da hakan ya fusatar da shi, Mista Wike ya zargi jam’iyyar da cin amanarsa da kuma keta kundin tsarin mulkinta.
Daga nan sai ya bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Iyorchia Ayu da ya yi murabus, kudurin da ya ce dole ne a cika shi kafin ya tattauna batun bai wa Atiku goyon baya a zaben 2023.
Hujjar da gwamnan Jihar Ribas din yake amfani da ita, ita ce, Mista Ayu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku, sun fito ne daga Arewa.
Binciken Aminiya ya gano cewar duk da kokarin da jiga-jigan Jam’iyyar PDP din suke tayi na ganin an dinke wannan baraka da zaben fid-da- gwani ya haifar ya faskara.
Haka rikicin ya kara cabewa ne, tun bayan da Atiku Abubakar ya bayyana sunan gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a takararsa, bayan da akayi tsammanin zai dauki gwamna Wike.
Wannan lamari na rashin daukar Wike ya harzuka wasu daga cikin mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar, inda har wasu suke ganin hakan da Atikun yayi bai dace ba, domin sai da shi Atiku ya ba wa mambobin kwamitin damar su ba shi shawarar cikin Wike da Okowa, wanda ya kamata ya dauka.
Mafi rinjanyen mabobin kwamitin sun amince da ya dauki Wike, amma Atiku yaki amincewa ya dauko Okowa, wanda hakan ya kara ruruta wutar rikicin da PDP ta tsinci kanta ciki.
Duk da cewar an ta bin hanyoyi don ganin an sasanta tsakanin Atiku da Wike, amma lamarin ya faskara.
Sai Ayu ya yi murabus —Wike
A cewar Wike, daga cikin sharudan da ya shimfida sun hada da shugaban jam’iyyar Ayu ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai kuma shugaban ya ki amincewa ya sauka daga mukamin nasa, wanda hakan har ta kai ga Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin ya sauka daga kan mukaminsa.
Wannan dai wai duk don a samu daidaito amma abin ya faskara tare da daukar sabon salo, ta inda wasu dake mara wa Wike baya suka maka Atiku da Jam’iyyar PDP da Hukumar Zabe kotu akan rushe zaben fi-da gwanin da ya kai Atiku ga zama dan takarar jam’iyyar.
A cewar gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom yace maganar gaskiya Jam’iyyarsu ta PDP tana cikin mawuyacin hali kuma komai na neman ya lalace.
Gwamnan ya ce rikicin da ke tsakanin Nyesom Wike, gwamnan Jihar Ribas da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, yana cutar da jam’iyyarsu.
Ya ce domin a dinke barakar da ke tsakanin Atiku da Wike, ya zama wajibi Jam’iyyar PDP ta dauki matakin da ya dace, don muddin aka ci gaba da hakan to wankin hula zai iya kai jam’iyyar dare.
Hakazalika, Gwamna Ortom ya ce duk wannan turka-turka da Jam’iyyar PDP ke fama da ita, ba kowa ne ya jawo ta ba sai shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu.
“Duk shi ne ya haifar da matsaloli da jam’iyyar ke ciki, wanda zai iya bawa jam’iyyar adawa hanyar ta ci gaba da rike mukami, muddin ba a fitar da wani tsari da zai magance rikice-rikicen cikin gida da ake da shi a yanzu.”
Adalci Wike yake son a yi —Ohuabunwa
Shi ma wani jigo a Jam’iyyar PDP, Sam Ohuabunwa, ya ce hakika gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas na neman a yi adalci ne kawai, ba wai yana kokarin kawo cikas ga jam’iyyar ba ne.
Mista Ohuabunwa ya bayyana haka ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels TV na Sunrise Daily ranar Talata.
Mista Ohuabunwa, wanda ya ce yana tattaunawa da tsagin Wike da Atiku a jam’iyyar, ya jaddada cewa gwamnan Ribas na neman gyara kura-kuran da aka yi a PDP a baya.
Duk da yake Walid Jibrin, Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP (BoT), ya yi murabus daga mukaminsa bisa zargin rashin daidaito a shugabancin jam’iyyar, Mista Wike ya dage cewa dole Mista Ayu ya ajiye mukaminsa domin jam’iyyar ta samu zaman lafiya.
Sai dai Mista Wike ya ce shugabancin kwamitin amintattu ba shi da muhimmanci kamar na shugaban jam’iyya.
Duk da wannan danbarwa da PDP take ciki ne, kuma a ranar 7 ga watan Satumba ne kwamitin zartarwar na Jam’iyyar PDP ya kada kuri’ar amincewa da Ayu, a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar, wanda hakan wata alama ce da zata hana Ayu yin murabus.
Sai dai Wike ya ce kada wannan kuri’a, tamkar shirin ba ci bane, kuma ya dage cewa ba za a yi sulhu ba har sai shugaban jam’iyyar ya sauka.
Dalilin da Wike ya cije —Fagge
Da yake zantawa da jaridar Aminiya, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero, Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana cewar matukar ba a samu daidaito ba tsakanin gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar ta PDP, Atiku Abubakar to tabbas hakan zai haifar musu da matsala, wadda za ta iya kaiwa ga rashin nasara a zaben 2023.
A cewarsa, irin wannan kalubale ne ya haifar wa Jam’iyyar PDP rashin nasara a zaben 2015 wanda kuma a yanzu hakan zai iya mai maituwa.
“Ba wai Jam’iyyar PDP ba, ko wacce jam’iyya ce idan tana fama da rigingimun cikin gida to bata iya tasiri a zabe.
“Don haka dangane da batun Atiku da Wike shima wannan abune wanda idan ba su yi kokari sun war ware shi ba to gaskiya zai iya jawowa Jam’iyyar PDP babbar asara.
“Na farko shi Wike duk da cewar gwamna ne kuma yana wa’adinsa na karshe, amma ya ba da gudummawa sosai wajen daukar nauyin jam’iyyar bama a jihar sa kadai ba har da sauran sassan kasarnan, shi ya sa yake da mabiya a cikin tafiyar.
“Ma’ana dai Wike jagora ne wanda yake da manyan mabiya. A don haka yin watsi da shi zai yiwa jam’iyyar illa.
“Abu na biyu bangaren da Wike yake wato Kudu maso Kudu bangarene wanda tunda aka dawo mulkin Dimokuradiyya a shekarar 1999, wuri ne da Jam’iyyar PDP take da karfi. Haka kuma Jihar Ribas tana wannan bangare.
“Don haka idan ba a gyara ba PDP za ta yi babbar asara daga wannan bangare. Duba da sauran bangarorin da tasirin sauran jam’iyyu a can, zai yi wuya PDP ta yi nasara idan har ta rasa Kudu maso Kudu.
“Idan ka koma Kudu maso Gabas akwai Peter Obi wanda shi ma zai samu kuri’u ma su yawa.
“Sannan a Kudu maso Yamma dama ba a tunanin PDP za tayi wani abu domin kuwa dan takarar APC daga wannan yankin yake.
“Idan ka dawo Arewa maso Gabas inda shi Atiku Abubakar ya fito, ba zai yi rawar gani a Borno da Yobe ba, tunda daga nan ne mataimakin dan takarar APC yake.
“Haka nan idan ka dawo Arewa maso Yamma nan ma akwai NNPP da APC kuma suna da tasiri a wannan yankin.
“Haka ma Arewa ta Tsakiya, nan kuma akwai Samuel Ortom, gwamnan Jihar Benuwe, wanda yana tare da Wike.
“Sai kuma Simon Lalong, gwamnan Filato wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman zabe na APC.”
Farfesa Fagge ya kara da cewa babu wata mafita ga Jam’iyyar ta PDP da dan takarar nata, wato Atiku Abubakar ta kowanne bangare, illa su dinke barakar da ke tsakaninsu, domin kuwa tafiya a hakan ba zai haifar musu da da mai ido ba a zaben 2023.
Ya kara da cewa babban abin da ya haifar da wannan rikici shi ne rashin kishi da siyasar ci gaba, inda ya ce dukkaninsu suna siyasa ce ta son kai da gina kawunan su ba don al’umma ba.
“Abin da ya sa wannan abu yaki-ci-yaki cinyewa a tsakaninsu saboda da Wiken da duk sauran ’yan siyasar Najeriya, suna siyasa ne ta son kai, ba siyasar akida bace, bata mutane bace, ba kuma siyasar kasa ba.
“Abin da ya sa shi Wike ya dage yana ganin idan har aka tafi a hakan to shi fa bangarensa an gama da shi a siyasance.
“Na biyu sun manta cewar shi fa Wike shi ya kawo tsohon shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus, wanda aka yi wa irin wannan aka cire shi.
“Ka ga dole ne shi ma a yanzu ya cije, ko don ya rama ko kuma don mutanen da suka yi ruwa da tsaki wajen cire shi su ji zafi,”inji Fagge.
Wike ya shigar da kara
Babbar Kotun Tarayya dai ta ware ranar 21 ga wannan wata na Satumba, domin sauraren karar da aka shigar gabanta, wanda tsagin gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya shigar yana kalubalantar yadda sakamakon zaben fid-da-gwani na Jam’iyyar PDP da ya samar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Mai shari’a Ahmed Mohammed ya sanar da ranar ga dukkan sassan biyu, da mai kara da kuma wadanda ake kara.
A karar da aka gabatar mai lamba: FHC/ABJ/CS/782/2022 wacce wani jigo a Jam’iyyar PDP, Cif Newgent Ekamon, ya shigar akan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar; da gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal.
Lauyan masu shigar da karar babban lauya, Arthur Obi Okafor (SAN), na bukatar kotu ta janye takarar Atiku, kuma ta bayyana Wike a matsayin dan takarar Jam’iyyar PDP, domin janyewar Tambuwal ta sa shi yayi asarar wasu kuri’un da yakamata ya samu.
Atiku dai ya samu kuri’u 371, inda Wike da Bukola Saraki suka sami kuri’u 237 da 70.