Atiku ne shugaban kasarmu a 2019 – Ministar Buhari

Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan ta nuna goyan bayanta ga Tsohon Mataimakin Shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar don zama shugaban kasa a zaben dake tafe na shekarar 2019. Ministar matan, wacce ta jagoranci shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Taraba domin kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Wazirin Aadamawa, Alhaji Atiku Abubakar a gidansa da […]

Atiku ne shugaban kasarmu a 2019 – Ministar Buhari

Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan ta nuna goyan bayanta ga Tsohon Mataimakin Shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar don zama shugaban kasa a zaben dake tafe na shekarar 2019.

Ministar matan, wacce ta jagoranci shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Taraba domin kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Wazirin Aadamawa, Alhaji Atiku Abubakar a gidansa da ke Yola, inda ta yi addu’ar Allah ya ba shi shugabancin Najeriya a 2019.

A wani faifan bidiyo da jaridar Aminiya ta samu a ranar Talatar da ta gabata, ya nuna ministar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasar tana mai cewa, “Mai girma, babanmu, shugaban kasarmu idan Allah ya yarda a shekarar 2019… a gabanka, mutanenka ne, magoya bayanka har abada; mutanen Jihar Taraba.”

Ta kuma cigaba da cewa “Sun zo gaisuwar ban-girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna ta wannan daukaka (Wazirin Adamawa) da Allah Ya kara maka. Domin daukaka Allah Ya riga Ya baka, to wannan kari ne, shi ne muka zo kuma muka tarar faduwa ta zo daidai zama, za a je godiya sai muka ce to dole ayi damu insha Allahu. To yanzu ga su nan, ga shugaban jam’iyya, shi ne shugabanmu, duk inda muka shi ne shugaban tawaga ni ‘yar jam’iyya ce, ga kuma mataimakin shugaba, Garba Chede, sga kodinatanka.”

Haka zalika Minista Aisha Alhassan ta gabatarwa tsohon mataimakin shugaban kasar shugabannin jam’iyyar, tana mai cewa “ Kowa yana cewa shi ma a bar shi ya dan fadi albarkacin bakinsa, amma na ce Baba ya gaji, ba lokaci, amma mai girma muna roko wadanda suka matsa – suka – matsa kadan kadan…”

Ministar ta harkokin mata dai ita ce ta yi takarar gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar APC a shekarar 2015, kodayake ta sha kaye a hannun Gwamna mai-ci, Darius Ishaku na PDP.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai fadar shugaban kasar ba ta ce kala kan faifan bidiyon da ya bayyana goyan bayan ministar matan ga tsohon mataimakin shugaban kasar ba. Kodayake Mai Taimaka wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a harkar sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ya bayyana cewa lallai akwai wadanda suke yi wa shugaban kasa zagon kasa a wannan mulki nasa, sai dai addu’o’in da ake ta yi masa ba zai sa yunkurin nasu ya yi tasiri ba.

Bashir ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook a wani dogon rubutu da ya yi a ranar Larabar da ta gabata. Inda ya ce addu’o’in talakawan Najeriya ne ke taimakawa wajen ruguza yunkurin masu yi wa shugaban kasar haka.

“Lalle akwai masu yi wa Baba Buhari zagon-kasa, amma addu’ar talakawa masoyansa kuma masoya Najeriya ba za ta taba bari yunkurinsu ya yi tasiri ba. Bayan samun lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari kamata ya yi mu tsaya da yi masa addu’o’in alheri ba domin akwai aiki mai dimbin yawa a gabansa akwai kuma mutane masu yawa da ba su fatan ganin ya yi nasara.

“Shugaba Buhari a kodayaushe fatansa shi ne ganin talakawa sun fita daga cikin kangin wahala, sun amfana da dukiyar da Allah ya hore wa kasarsu Najeriya, amma irin wadanna mutane burinsu shi ne a kullum su ga talakawa na kara fadawa cikin wahalhalun rayuwa, wannan dalili ya sa suka yi damarar yaki da Baba Buhari, yakin da ba za su yi nasara ba.

“Martanin Baba Buhari a yau kan labarin fitar Najeriya daga kadamin kangin tattalin arziki shi ne, ya nuna farin cikinsa da nasarar da aka samu, amma sai ya ce aiki ko kadan bai kare ba har sai lokacin da talakawa suka tabbatar da hakan ta hanyar samun saukin yadda suke tafiyar da rayuwar su ta yau da kullum. Zan yi amfani da wannan dama in roki ‘yan Najeriya musamman masoya Baba Buhari da mu ci gaba da sa shi cikin addu’o’inmu kan Allah Ya ba shi nasara kan duk wasu masu yi wa gwamnatinsa zagon-kasa na fili da na boye,” in ji Bashir Ahmad.

Masana harkokin siyasa dai na ganin tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya fafata da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fitar da gwani na APC a shekarar 2014, zai sake tsayawa takara a zaben 2019.

Haka kuma suna ganin wannan ce dama ta karshe ga Alhaji Atiku Abubakar ta zama shugaban kasar, ganin cewa har yanzu ana tunanin za a fitar da shugaban kasar ne daga yankin Arewa, sannan shekarunsa na ci gaba da ja, inda a yanzu haka ya haura shekara 70.

Sai dai suna ganin zai fuskanci babban kalubale a wurin mutane irinsu tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin na APC a wancan lokaci kuma ake tunanin zai sake son tsayawa takara, da gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, wadanda baki dayansu ake ganin za su nemi kujerar shugabancin kasar.

Kazalika masana siyasa na ganin Atiku Abubakar zai fuskanci adawa daga tsohon maigidansa Cif Olusegun Obasanjo, wanda ake ganin har kawo yanzu ba sa ga-maciji da juna.

Sun bayyana cewa rashin lafiyar da Shugaba Buhari, mai shekara 74, ke fama da ita, na cikin abubuwan da ke kara kaimi ga masu son yin takara a zaben 2019 su fito su bayyana hakan da zarar ya ce ba zai sake yin takara ba. Amma har yanzu shugaban bai bayyana manufarsa ta sake tsayawa takarar ko akasin hakan ba. Amma makusantansa sun nuna yiwuwar tsayawa takararsa a shekarar 2019.