Atiku ya bar jam’iyyar APC zuwa ta PDP?

…“Bayan neman zabin Allah da kuma shawara da iyalina, da magoya bayana da sauran mutanen Najeriya da na hadu da su a wurare da lokuta daban-daban, Ni, Atiku Abubakar wazirin Adamawa ina bayyana barina jam’iyyar APC, lokacin da zan yi nazari akan makomata. Allah Ya albarkace ku Allah Ya albarkaci Najeriya.” Wadannan kalamai na daga […]

Atiku ya bar jam’iyyar APC zuwa ta PDP?

…“Bayan neman zabin Allah da kuma shawara da iyalina, da magoya bayana da sauran mutanen Najeriya da na hadu da su a wurare da lokuta daban-daban, Ni, Atiku Abubakar wazirin Adamawa ina bayyana barina jam’iyyar APC, lokacin da zan yi nazari akan makomata. Allah Ya albarkace ku Allah Ya albarkaci Najeriya.” Wadannan kalamai na daga cikin kalaman da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ambata a cikin wata takardar da ya sanya wa hannu da kansa, ya kuma aika wa shugabancin jam’iyyar APC na kasa baki daya a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja. Samuwar hakan ya kawo karshen rade-radin da aka dade ana yi a kasar nan a ‘yan watannin nan na cewa tsohon mataimakin shugaban kasa zai bar jam’iyyarsu ta APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP. 

Ba zai zama abin mamaki ba idan aka ce Atikun ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, inda kuma ake sa ran ya samu cikasa burinsa na neman takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019, kasancewar rahotanni sun tabbatar da cewa akasarin shugabanni da wakilai da aka zaba a tarurrukan mazabu da kananan Hukumomi da jihohi na jam’iyyar PDP da aka yi a kwanakin baya magoya baya ko masoyan Wazirin Adamawa ne. Dadin-dadawa a ‘yan watannin baya ne aka ji Ministar Al’amurrar mata Sanata Aisha Jummai Alhassan da aka fi sa ni da Maman Taraba da ta tsayawa jam’iyyar APC takarar neman Mukamin Gwamnan Jihar Taraba a zaben 2015, ana cewa idan har Atiku Abubakar ya bar APC ya koma kowacce jam’iyya, to kuwa ba makawa za ta bi shi ta mara masa baya kasancewarsa ubangidanta tun ma ba ta shigo siyasa ba, ta na mai cewa ita ba munafuka ba ce. Shi ma Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Jibrilla Bindow ya taba fadin cewa ya na tare da Atiku duk inda zai shiga. 

Idan mai karatu zai koma baya ya yi nazari, Atiku na daya daga cikin gagga-gaggan ‘yan siyasar kasar nan, tun daga lokacin da gwamnatin soja ta shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai (ritaya) ta nuna aniyar za ta mika mulki hannun farar hula. Wannan ta sanya shekarar 1993, Atiku ya tsaya takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar SDP, amma ya zo na uku bayan marigayi Cif M.K.O Abiola da kuma Ambasada Babagana Kingibe. Kasancewar Atiku yana da babban hannun damar marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar aduwa, ya sanya ya gaji dukkan tsari da magoya bayan Janar ‘Yar aduwa, ta yadda bayan mutuwarsa, Atikun ne ya zama kwamanda Janar na tafiyar tsarin siyasar marigayin, wannan ta sanya duk da a zaben 1999, Atikun ya tsaya takarar neman gwamnan jiharsa ta Adamawa a inuwar jam’iyyarsu ta PDP da ya ke cikin manyan ‘yan siyasa 34, da suka kafa PDP da kuma tunawa da marigayi Shehu ‘Yar aduwa ta sanya Cif Olusegun Obasanjo ya dauko shi ya ba shi mataimakinsa, inda da dadi da ba dadi suka share shekaru 8, su na mulki da Shugaba Obasanjo. Waccan dama da Wazirin Adamawar ya samu ta kara ba shi damar fadada tsarinsa na siyasa da ya game kasa baki daya, abin da ya kawo zuwa yanzu daya da daya ba ka da dan siyasar da ke da tsari da manya manyan ‘yan siyasa a dukkan fadin kasar nan. 

A cikin yunkurinsa na ya cimma burinsa na zama shugaban kasar nan ta sanya yanzu daya da daya ba wanda ya zama karuwar siyasa irinsa a cikin manya manyan ‘yan siyasar kasar nan. Alal misali ka dauka koda daga 1999, wato farkon wannan jamhuriyar bayan Wazirin Adamawan ya shiga ACN, ya kuma koma PDP, sannan ya kafa PDM ta bayan gida, sannan ya tsallako ya koma APC, yanzu kuma ga shi ya bar APC ana rade-radin PDP zai sake dosa, duk a kokarin sai ya zama shugaban kasa. Yanzu dai maganar da ake a ranar 25-11-2017, Atikun ya cika shekara 71 daidai a duniya, idan har Allah Ya ba shi mulki a shekarar 2019 lokacin zai kasance yana dan shekaru 73, ke nan a duniya. 

Masu iya magana kan ce “Himma ba ta ga Raggo”, wasu kuma su ce “Duniya ba ta Raggo ba ce.” Dukkan wannan yunkurin neman kai ga biyan bukata da Wazirin Adamawa ya ke suna kan hanya a zaman shi na dan Adam, kuma dan kasar nan da ke da ikon ya nemi dukkan mukamin da ya ke bukata, amma wasu na ganin tamfar ya zaku ne akan ta kowane hali sai ya yi shugabancin kasar nan, amma a makon jiya an ruwaito Daraktan gamayyyar magoya bayansa Malan A A Lawan yana fadi a Abuja cewa gwanin nasa ba zakuwa ya yi ba akan sai ya mulki kasar nan, illa dai yana son ya ceto kasar nan daga koma bayan rashin ci gaban da take fama da shi. Yana mai cewa an san shi Atikun mai kudi ne kuma ya shahara a harkokin kasuwanci, don haka matsalarsa ba ta ya tara kudi ba ce, so kawai ya ke ya bauta wa jama’a. 

Maganar da ake dai yanzu an jiwo Kakakin jam’iyyar PDP na kasa baki daya Yarima Dayo Adeyeye yana fadin cewa suna maraba da Atiku ya shigo jam’iyyarsu, amma kuma ya kwan da sanin cewa jam’iyyar ba za ta ba shi takarar neman shugabancin kasar nan kai tsaye ba, sai ya bi dukkan tanade-tanaden da kundin tsarin mulkinta suka tanada. Su ma ‘yan takarar neman shugabancin kasa na jam’iyyar ta PDP da zuwa yanzu suka bayyana aniyarsu ta neman wannan takara, irin su tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan ilmi Malam Ibrahim Shekarau da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da tsohon shugaban majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark da shi kanshi shugaban kwamitin riko na kasa baki daya na jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Muhammad Makarfi da ake zargin yana cikin masu neman takarar shugabancin kasa, sun ce suna maraba da dawowar Atikun in har zai dawo cikin PDP, amma ko kusa ba sa fargabar su fafata da shi muddin jam’iyya za tai adalci. 

A duk cikin jiga-iigan PDP da su ka furta ta albarkacin bakunan su akan dawowa da neman takara shugabancin kasa na Atikun, a gani na tsohon shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan kadai na ga ya yi wata muhimmiyar magana, inda ya ke shawartar Atikun ya lallai muddin yana son ya kai ga nasara, to kuwa ya nemi sulhuntawa da tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo. Obasanjon da Dokta Jonathan ya ce ba abin watsi ba ne ga dukkan wanda ke son kai ga nasara wajen samun nasarar cin shugabancin kasar nan. Ko shakka babu Dokta Jonathan yana magana ne bisa ga irin hujjojin da ya ke da su, na abin da ficewar Cif Obasanjo daga jam’iyyar PDP gab da zaben 2015, su suka ja za masa faduwar da ya yi a wancan zabe, kuma daga wancan lokaci jam’iyyar PDP ta afka cikin kogin rigingimu da sai a ‘yan watannin nan ake ganin za ta fita daga cikinsu, bayan samun nasarar babban taronta na kasa da za ta yi a karshen makon gobe. Saura da me? 

Lallai Wazirin Adamawa ya kara sa ni cewa kalubale da ke gabansa ba karami ba ne, don kuwa bayan na cikin gida da zai fuskanta idan har ya koma PDP, to kuma akwai na Shugaba Muhammadu Buhari, Buharin da har gobe talakawan Arewacin kasar nan da ma na sauran sassa suna tare da shi.