Atiku ya caccaki Tinubu kan rikicin BCDA

Atiku yana mai cewa, hakan ya nuna gazawar gwamnati wajen tafiyar da harkokinta.

Atiku ya caccaki Tinubu kan rikicin BCDA

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye Hukumar Raya Yankunan Kan Iyakokin Najeriya (BCDA).

Atiku yana mai cewa, hakan ya nuna gazawar gwamnati wajen tafiyar da harkokinta.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar Atiku ya ce abin kunya ne yadda aka sanar da naɗin sabon Babban Sakataren Hukumar BCDA, amma wanda aka ce an maye gurbinsa ya ci gaba da gudanar da aikinsa.

Ya ce, rikicin BCDA ya ƙara fito da abin da ya kira matsalolin da suka addabi gwamnatin Tinubu wajen gudanar da hukumomin gwamnati, yana mai cewa irin waɗannan rikice-rikice na rage amincewar jama’a da kuma ta masu zuba jari.

Atiku ya kuma buƙaci Fadar Shugaban Ƙasa ta fayyace matsayin shugabancin BCDA tare da tabbatar da cewa, duk naɗe-naɗen gwamnati suna bin tanadin doka.

An gurfanar da wanda ya kashe matarsa da ƙona gida

Atiku ya caccaki Tinubu kan rikicin BCDA

An kama ’yan Togo biyu kan shirin garkuwa da mutum

’Yan bindiga sun sace ’yan gudun hijira a Sakkwato