Atiku ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna

Atiku ya ci kananan hukumomi 14 cikin 23 na Jihar Kaduna, APC ta samu biyu, duk da zaman Gwamna El-Rufai dan a-mutun Tinubu

Atiku ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar adawa ta PDP, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zabe a Jihar Kaduna.

Atiku ya lashe zaben ne, duk da kasancewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dan a-mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Tinubu.

Baturen zaben, Farfesa Muhammad Zayyan Umar, ya sanar da cewa Atiku ya yi nasara da kuri’u 554,360.

Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 399,293, LP ta zo na uku da kuri’u, sannan NNPP  92,962.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi nasara a 14 daga cikin kananan hukumomi 23 da ke Jihar Kaduna.

Jam’iyyar LP ta lashe kananan hukumomi bakwai a yayin da APC mai mulkin jihar ta ci kananan hukumomi biyu.

Alkaluma:

  • Masu rajistar zabe – 4,335,208
  • Mutanen da aka tantance – 1,418,046
  • Kuri’un da aka kada – 1,401,376
  • Kuri’u masu kyau – 1,360,153
  • Lalatattun kuri’a – 41,223