Atiku ya gana da shugabannin CAN
Atiku ya ce dole ne ya tuntubi masu ruwa da tsaki kan tafiyarsa.
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Abuja.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar wanda ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa a Twitter, ya ce taron ya gudana ne a cibiyar Ecumenical da ke Abuja.
- Hatsarin mota: Gombawa 17 sun rasu a hanyar zuwa Legas
- 2023: Kotu ta umarci INEC ta ci gaba da rajistar masu zabe
Ya rubuta cewa, “Don mu dawo da Najeriya, muna bukatar tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a kasarmu.
“Na halarci cibiyar Ecumenical da ke Abuja don tattaunawa da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).”
Tun ba yanzu ba dai Atiku ya yi alkawarin tattaunawa da shugabannin na CAN domin tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki wajen nema wa Najeriya mafita.
Ana iya tuna cewa, a ranar 16 ga watan Nuwamba 2022 ne, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya gana da shugabannin CAN, inda suka tattauna kan batun zabar musulmi da musulmi a 2023.
A yayin ganawar, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa idan aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, gwamnatinsa za ta yi tafiya tare da kowa ba tare da la’akari da bambancin addini ba.