Atiku ya kalubalanci masu alakanta shi da cin hanci

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalenci wadanda ke ci gaba da alakanta shi da zargin cin hanci da rashawa su kawo hujjar da ta nuna ya taba cin hanci da rashawa a lokacin ya na gwamnati. Atiku ya shawarci ’yan siyasar da ke gaba da shi cewa idan ba za su iya […]

Atiku ya kalubalanci masu alakanta shi da cin hanci

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalenci wadanda ke ci gaba da alakanta shi da zargin cin hanci da rashawa su kawo hujjar da ta nuna ya taba cin hanci da rashawa a lokacin ya na gwamnati.
Atiku ya shawarci ’yan siyasar da ke gaba da shi cewa idan ba za su iya kawo hujjar da ta nuna ya taba cin hanci ba to su yi shiru da bakinsu su mayar da hankali kan matsalolinsu.
Jigo a jam’iyyar APC ya yi furucin ne jiya yayin da ya kai ziyarar gani da ido a sabon ginin kamfanin dab’i na Yaliam da ke yankin Jabi a Abuja.
A wata sanarwa da ofishinsa da ke kula da harkokin yada labarai ya fitar a Abuja ta nuna cewa Atiku zai yaki cin hanci yadda ba a taba yi ba a tarihin kasar muddin aka bashi damar jan ragamar mulkin kasar.