Atiku ya lashe zaben dan takarar shugaban kasar PDP

Atiku ya yi wa ragowar masu neman takarar shugaban kasa a PDP fintinkau

Atiku ya lashe zaben dan takarar shugaban kasar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaba Kasa, Atiku Abubakar, ya zama dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Atiku ya samu tikitin ne bayan ya samu mafi rinjayen kuri’u a zaben fitar da dan takarar da jam’iyyar ta gudanar a ranar Asabar, 28 ga Mayu, 2022.

A karshen zaben, Atiku ya samu kuri’a 371, sai mai bi mishi, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da kuri’a 237.

“A yau mun fara aikin sake ginawa da kuma hada kan wannan hamshakiyar kasa; Ina alfahari da aka sanar da ni a matsayin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.

“Ina fatan tattaunawa da daukacin ’yan Najeriya domin isar da sakon kyakkyawan fata da kuma hadin kai a yunkurinmu na sake gina rayuwarmu ta goba a matsayin al’umma daya,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Alkaluman da alkalan zaben suka fara sanarwa sun nuna an samu kuri’a 12 da suka lalace, sai kuma ‘yan takara da suka samu kuri’u kamar haka.

  1. Olivia Tariela – 1
  2. Pius Anyim – 14
  3. Bala Mohammed  – 20
  4. Udom Emmanuel – 38
  5. Bukola Saraki – 70
  6. Nyesom Wike – 237
  7. Atiku Abubakar – 371.

A jawabin godiyar ga magoya bayansa bisa mara masa baya da suka yi wajen lashe zaben fidda gwani, Atiku ya ce muddin ya zama shugaban kasa, hadin kan kasa, fannin tsaro da kuma tattalin arziki na daga cikin bangarorin da zai fi bai wa muhimmanci.

Tuni magoya bayan dan takarar suka shiga sowa da murna tun baya da suka ga ya yi wa sauran ‘yan takara fintikau a lokacin kirgen kuri’un da aka jefa.

Daliget 766 ne suka jefa kuri’a daga cikin 767 da aka tantance a taron da ya gudana a Babban Filin Wasa na MKO Abiola da ke Abuja.

Mutum kimanin 11 ne suka fafata a zaben, inda Atiku ya yi musu fintinkau, da fiye da rabin kuri’un da aka jefa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno