Atiku ya nemi Tinubu ya binciki zargin kafa hukumar bogi a Najeriya
Atiku ya ce bincike ne kaɗai zai tabbatar da ainahin masu hannu a kafa hukumar .
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa kan ce-ce-ku-cen zargin kafa wata hukumar bogi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Atiku ya ce batun ya wuce zargin jabun takardu.
- Kotu ta sanya 22 ga Yuli don kammala sauraron shari’ar takarar Sanatan APC a Gombe
- Mutum 18 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Neja
A cewarsa, abin tambaya shi ne yadda wata hukuma da Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu ita ta samu shiga cikin bayanan gwamnati tare da gudanar da wasu ayyuka.
Ya bai wa Shugaba Tinubu wa’adin kwana bakwai da ya sa a yi bincike tare da bayyana sakamakonsa ga jama’a.
Ya ce rashin yin hakan zai ƙara jefa shakku cewa wasu masu ruwa da tsaki a gwamnati na da hannu ko kuma kare waɗanda ake zargi.
Atiku, ya tambayi yadda ake zargin hukumar ta samu ofishi, ta yi hulɗa da jami’an gwamnati da jakadun ƙasashen waje, ta bayyana a cikin kasafin kuɗin 2026.
Sannan ya nemi yadda aka amince ta ɗauki ma’aikata sama da 300, alhali Fadar Shugaban Ƙasa na cewa ba hukumar gwamnati ba ce.
Ya kuma ce mutumin da ake zargi da hannu a kafa hukumar ya musanta aikata laifin tare da zargin cewa wasu manyan mutane na ƙoƙarin rufe masa baki, abin da ya sa ya zama dole a gudanar da bincike mai zaman kansa.
Atiku, ya ce bincike ne kaɗai zai iya gano gaskiyar lamarin, ya fallasa duk masu hannu a ciki, tare da dawo da amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati.