Atiku ya soki lamirin gwamnatin Buhari
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya soki lamirin gwamnatin Shugaba Buhari inda ya yi korafin ba a damawa da shi a gwamnatin. Atiku ya yi furucin ne a tattaunawar da ya yi da gidan rediyon Muryar Amurka a garin Yola da ke jihar Adamawa a jiya. Ya ce gwamnati ta mayar da shi […]

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya soki lamirin gwamnatin Shugaba Buhari inda ya yi korafin ba a damawa da shi a gwamnatin.
Atiku ya yi furucin ne a tattaunawar da ya yi da gidan rediyon Muryar Amurka a garin Yola da ke jihar Adamawa a jiya.
Ya ce gwamnati ta mayar da shi saniyar-ware shi ya sa shi ma ya koma gefe daya yana kallon ikon Allah.
“Ba a taba tuntubata ba a kan wata shawara. Ni ma da na ga haka sai na koma gefe ina kallonsu”. Inji shi.
Atiku ya yi ikirarin cewa gwamnatin Buhari ta ajiye shi a gefe duk da dimbin dukiyar da ya kashe tare da yin amfani da magoya bayansa wajen kayar da jam’iyyar PDP.