Atiku ya taya Mahama murnar lashe zaɓen Ghana
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya aike da saƙon taya murna ga, John Dramani Mahama, kan nasarar lashe zaɓen ƙasar Ghana.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya aike da saƙon taya murna ga, John Dramani Mahama, kan nasarar lashe zaɓen ƙasar Ghana.
Saƙon Atiku na zuwa ne bayan ɗan takarar jam’iyyar NPP mai mulkin Ghana, Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye, tare da taya John Mahama murna.
- Tinubu ya taya Mahama murnar lashe zaɓen Ghana
- Yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ta faranta wa mazauna Birnin Gwari
Atiku ya ce, “Ina miƙa saƙon taya murna kan nasarar da ka samu, mai girma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana, John Mahama,” in ji shi.
Duk da haka, har yanzu hukumar zaɓen ƙasar Ghana ba ta sanar da sakamakon zaɓen kai-tsaye ba, amma alamun nasara sun fara bayyana ga Mahama.
Wannan na nuna alamar juyin-juya hali a siyasar Ghana, inda al’ummar ƙasar ke fatan samun jagoranci na gari.
Shugabannin duniya na ci gaba da taya Mahama murnar samun nasarar lashe zaɓen ƙasar mai cike da tarihi.