Atiku ya yi takaicin sake karyewar arzikin Najeriya

Sau biyu ke nan tattalin arzikin Najeriya yana durkushewa a cikin shekara biyar.

Atiku ya yi takaicin sake karyewar arzikin Najeriya

Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya bayyana takaicinsa kan sake durkushewar tattalin arzkin Najeriya da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar.

A ranar Asabar ce hukumar ta fitar da sabon rahoton da ke cewa tattalin arzikin kasar ya sake durkushewa.

“Na kadu matuka da samun rahoton sake karyewar tattalin arzikin a karo na biyu cikin shekara biyar”, inji Atiku ta shafinsa na Twitter.

NBS ta ce tattalin arzikin Najeriya ya ragu da kaso 3.62% a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020.

Karyewar tattalin arzikin na nufin yiwuwar kara tabarbarewar al’amuran rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi.

Sauran sun hada da karancin kudin biyan bukatu, rashin ayyukan yi da durkushewar masana’antu.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta