Atiku ya yi wa Tinubu jajen auna tsautsayi a Eagle Square
Ba wai kawai Shugaba Tinubu ba, duk wanda ke raye zai iya zamewa ya faɗi, in ji Shehu Sani.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya jajanta wa Shugaba Bola Tinubu dangane da auna tsautsayin da ya yi a wannan Larabar.
Aminiya ta ruwaito faɗuwar da shugaban ƙasar ya yi a wurin bikin Ranar Dimokuradiyya a dandalin Eagle Square da ke birnin Abuja a yau Laraba.
- Erik Ten Hag zai ci gaba da zama a Manchester United
- HOTUNA: Yadda aka gudanar da bikin Ranar Dimokuradiyyar Najeriya
Shugaba Tinubu ya faɗi ne a yayin hawa motar da za ta zagaya da shi domin kallon fareti a dandalin Eagle Square a safiyar Larabar nan.
Nan da nan haɗimansa da wasu sojoji suka kewaye shi domin ɗaga shi, kuma nan take shugaban ya murmure har ya fara ɗaga wa jama’a hannu a yayin da motar da fara zagayawa da shi a dandalin na Eagle Square.
Hoton bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna Tinubu sanye da farar babbar riga yana ƙoƙarin dafa motar don kare kansa daga faɗuwar.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Atiku ya yi wa Tinubu fatan kasancewa cikin ƙoshin lafiya bayan aukuwar wannan lamarin.
“Ina mai matuƙar jajanta wa shugaba Bola Tinubu kan mummunan abin da ya faru da shi a daidai lokacin da yake ƙoƙarin fara kallon faretin Ranar Dimokuraɗiyya. Ina fatan yana cikin ƙoshin lafiya.”
Kazalika, tsohon wakilin Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani da ya bayyana nashi alhinin cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin X.
“Ba wai kawai Shugaba Tinubu ba, duk wanda ke raye zai iya zamewa ya faɗi; hakan ya faru da Shugaba Biden da Fidel Castro. Shugabanni mutane ne kamar kowa” in ji sanata Shehu Sani
Hoton bidiyon yadda shugaban ya zame, ya haifar da cece kuce da muhawarori a dandalan sada zumunta da dama, inda mafiya wasu ke tausayawa da jajanta wa shugaban yayin da wasu ke nuni da sabanin haka.