Atiku zai garzaya kotu kan zaben shugaban kasa

Atiku, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa, ya ce zaben 2023 shi ne mafi muni a tarihin Najeriya

Atiku zai garzaya kotu kan zaben shugaban kasa

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 da aka gudanar a ranar Asabar a kotu.

Atiku, a wani taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce matakin bai shafe shi ba kai-tsaye, amma zai yi haka ne don dimokuradiyyar Najeriya.

“Zaben da aka gudanar a karshen mako babu gaskiya a cikinsa. Binciken farko ya nuna cewa shi ne zabe mafi muni da aka taba gudanarwa tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.

“Magudi da zamba da aka yi a wannan zaben, ba a taba yin irinsa ba a tarihin kasarmu.

“Na kasa fahimtar dalilin da ya sa aka yi gaggawar bayyana sakamakon zaben duk da korafe-korafen da aka yi game da shi,” in ji shi.

Ya ce tuni ya tuntubi shugabannin jam’iyyarsa ta PDP da ’yan Najeriya daga bangarori daban-daban kan sakamakon zaben, kuma suka cimma matsayar garzaya wa kotu.

Atiku ya ce masu sanya ido na cikin gida da na waje sun tabbatar da akwai kura-kurai a zaben.

Ya ce ya yi imanin cewa wannan ba shi ne alkawarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ba, kuma bai makara ba ya gyara barnar da aka yi a zaben.

Atiku Abubakar ya zo na biyu a zaben da aka gudanar bayan shan kaye a hannun Tinubu na jam’iyyar APC.