Atiku zai iya kamfen a filin wasa na Sani Abacha- Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, zai iya amfani da filin wasa na Sani Abacha don gudanar da yakin neman zabensa shugaban kasar Najeriya. A ranar Lahadi 10 ga watan Fabirairu 2019 ne, jam’iyyar PDP ta tsara a matsayin ranar kamfen […]
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, zai iya amfani da filin wasa na Sani Abacha don gudanar da yakin neman zabensa shugaban kasar Najeriya.
A ranar Lahadi 10 ga watan Fabirairu 2019 ne, jam’iyyar PDP ta tsara a matsayin ranar kamfen dinsa a jihar Kano, amma gwamnatin Kano ta bayar da umarnin rufe harabar da zasu yi taron don yin wasu gyare-gyare da ta ce za a yi.
Daga bisani Kwamishin watsa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanar da cewa, Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya umarci ‘yan kwangilan da zasu yi aikin filin wasan da su baiwa jam’iyyar PDP damar amfani da harabar don gudanar da taron su.