Atiku zai kama barayin Gwamnatin Buhari idan ya zama shugaban Kasa – PDP
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa dan takararta na Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar zai garkame barayin gwamnatin Buhari idan lashe zaben 2019. Jam’iyyar PDP ta ce, Atiku zai kaddamar da shirin yaki da cin hanci da rashawa idan ya lashe zaben kuma zai sake karfafa wa hukumar da ke yaki da masu […]
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa dan takararta na Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar zai garkame barayin gwamnatin Buhari idan lashe zaben 2019.
Jam’iyyar PDP ta ce, Atiku zai kaddamar da shirin yaki da cin hanci da rashawa idan ya lashe zaben kuma zai sake karfafa wa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya, EFCC gwiwa da wasu hukumomi don tabbatar da doka.