Atiku zai takarar Shugaban kasa a zaben 2015
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben da za a gudanar a badi a karkashin Jam’iyyar APC.Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba a Abuja a gaban cincirindon magoya bayansa.Wannan ne karo na uku da Atiku wanda tsohon dan Jam’iyyar PDP ne da ya […]
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben da za a gudanar a badi a karkashin Jam’iyyar APC.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba a Abuja a gaban cincirindon magoya bayansa.
Wannan ne karo na uku da Atiku wanda tsohon dan Jam’iyyar PDP ne da ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC zai tsaya takarar nema kujerar Shugaban kasa.
Atiku wanda ya tsaya takarar a karkashin Jam’iyyar ACN da PDP ya koma APC bayan da ya yi zargin cewa ba a yi masa adalci a PDP ba.
Wannan aniya ta Atiku ta zo ne a daidai lokacin da jiga-jigan Jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Yamma suka yanke shawarar goya masa baya a wannan yunkuri nasa.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a Cibiyar Shehu Musa ’Yar’aduwa da ke Abuja, inda ya kira taron manema labarai na duniya, Atiku ya bayyana kudirinsa da na Jam’iyyar APC na ba ’yan Najeriya kyakkyawan shugabanci da suke fata, shugabancin da zai kauce wa almundahana tare da kawo sauyi nagari.
“Ina son jagorantar wata gwamnati wadda ba za ta lamunci almudahana da rashawa ba, wadda za ta taimaki Najeriya ta hau kan matsayinta a duniya,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Wannan kira ne da na zo amsawa. Kuma tare da goyon baya da addu’ar ’yan Najeriya za mu gina wata babbar sabuwar Najeriya ga ’yan Najeriya.”
Ya bukaci matasa su shiga a dama da su a harkokin zabe, inda ya ce su ne manyan gobe da makomar kasar nan take hannunsu. “Ku ne madogarar wannan kasa. Zaben 2015 dominku ne,” ya shaida wa matasan.
Sai ya yi shagube ga gwamnatin Shugaba Jonathan cewa, makomar kasar nan ba zai ci gaba da zama kan gwaji ko koyo kullum ba.
“Siyasata ta ginu ne kan adalci da daidaito. Ina da kwarewar da zan tafi da dukkan jama’a mu gyara al’amura. Muna bukatar kakkarfan shugabanci da zai samar da aikin yi. Kuma da goyon bayan ’yan Najeriya, APC za ta kafa gwamnati a shekarar 2015. Kuma na yanke shawarar in nemi tsayawa takara a karkashin APC don tsayawa takarar Shugaban kasa,” inji shi.
Wannan ne karo na hudu da Atiku zai tsaya takarar Shugaban kasa, inda ya gaza samun nasara a yunkuri uku na farko.
Ya fara tsayawa takara ne a 1992 inda ya sha kasa a zaben fidda gwani a hannun marigayi Cif MKO Abiola a karkashin Jam’iyyar SDP. A shekarar 2007, ya zo na uku a bayan Shugaba Jonathan da Janar Muhammadu Buhari, lokacin da ya tsaya takara wa Jam’iyyar AC. Sai a shekarar 2011 ya fadi a zaben fidda gwani na PDP, kafin ya koma APC.