Yau Atiku zai yi wa duniya jawabi kan Takardun Tinubu da Jami’ar Amurka ta fitar
A karon farko Atiku zai yi jawabi kan takardun shaidar karatun Shugaba Tinubu da Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ta fitar.
A yau ne dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar zai yi jawabi a karon farko kan takardun shaidar karatun Shugaba Tinubu da Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ta fitar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar zai bayyana matsayinsa ne a wani taron ’yan jarida na kasa da ya kira, kan takaddamar takardun Tinubu.
- Taurarin Zamani: Al-Ameen G-Fresh
- Abin da ya sumar da ni a wurin tantancewa —Ministan da ya maye gurbin El-Rufai
- Jami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu
Tun bayan fitar da takardun shaidar karatun na Tinubu aka fara sabon ta ce-ce-ku-ce, inda wasu ke cewa magana ta kare, wasu kuma ke cewa akwai takardun da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sun sha bamban da wadanda jami’ar ta fitar.
Tambari da kuma bajon da jami’ar ta saki na takardun digirin 1977 sun yi daidai da na wadanda Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu bambanci a kwanan wata.
Amma cikin wani bayanin da ta yi jami’ar ta dauki alhakin kuskuren rubutu da ta yi a kwanan watan.
Sai dai kuma ta bayyana cewa ba ta da kwafin takardar shaidar diflomar da Tinubun ya gabatar, kuma ta yi duk iya bincikenta ba ta gani ba, saboda takardar diflomar aba ce ta al’ada da ta kebanci dalibi amma jami’ar ba ta ajiye kwafi.
Atiku dai na zargin takardun da Tinubu Jami’ar (CSU) ke amfani da su na bogi ne, wanda a bisa haka ne yake neman kotu ta soke nasarar Tinubu ta ayyana shi a matsayin shugaban kasa.
A farkon makon nan ne Jami’ar CSU ta fitar da kwafin takardun shaida da bayanan karatun na Tinubu a bisa umarnin kotun da tsohon mataimakin shugaban kasar ya shigar da kara.
Atiku ya shigar kara a kotun ne yana neman ta umarci jami’ar da Tinubu ke ikirarin halarta umarnin fito da takardun shaidar karatun.
Da farko CSU ta tabbatar cewa Tinubu tsohon dalibinta ne amma ba ta da hurumin fitar da bayanan karatun, saboda abubuwa ne da suke kebanci alfarmarsa, sai dai idan kotu ce ta ba da umarni.