Attajirai 80 ne suka mallaki dukiyar rabin al’ummar duniya

Hamshakan attajiran duniya 80 sun mallaki yawan dukiyar rabin al’ummar duniya, kamar yadda biniciken Odfam ya nuna, sabanin yadda a shekarar 2010, inda sai an tattara attajirai 388, wadanda suka mallaki biliyoyin dalar Amurka sannan a samu kimar wadanda suka mallaki rabin arzikin duniya. Kashi daya cikinj 100 na wadannan hamshakan attajirai, sun samu habakar […]

Attajirai 80 ne suka mallaki dukiyar rabin al’ummar duniya
Attajirai 80 ne suka mallaki dukiyar rabin al’ummar duniya

Hamshakan attajiran duniya 80 sun mallaki yawan dukiyar rabin al’ummar duniya, kamar yadda biniciken Odfam ya nuna, sabanin yadda a shekarar 2010, inda sai an tattara attajirai 388, wadanda suka mallaki biliyoyin dalar Amurka sannan a samu kimar wadanda suka mallaki rabin arzikin duniya.

Kashi daya cikinj 100 na wadannan hamshakan attajirai, sun samu habakar arziki ne cikin shekaru biyar da suka gabata, kamar yadda Mujallar Forbes ta jero su, a cewar kungiyar jinkai Odfam. A shekara 2010, wadancan masu kudi 80 na duniya yawan dukiyarsu bai wuce a kimanta ta a kan tiriliyan daya da biliyan 300 ba. Sai kawai ga shi a shekarar da wuce, kimar dukiyarsu ta kai tiriliyan daya da biliyan 900, al’amarin da ke nuni da cewa, sun samu karuwar Dalar Amurka biliyan 600.
In an tara dukiyar wadannan kashi guda cikin 100 na hamshakan attajirai aka hada da na wasu kashi 48 cikin 100 na masu kudin duniya bisa alkaluman kididdigar binciken shekarar 2014, shi ya tabbatar da cewa sun mallaki kashi 50- cikin 100 na duniyar daukacin mutanen duniya.
Wannan bincike na kungiyar agaji ta Odfam yana shan suka, saboda masana na ganin sun tara yawan kadara ce kawai, amma ba su yi la’akari da nauyin da ke kan dukiyar ba, wadanda suka hada da bashi. Wata sukar lamirin binciken ta nuna cewa, tara dukiyar talakawan duniya ba shi da wata ma’ana, saboda talakawa dai matalauta ne ko suna da kadarori kadan da basussuka in an kwatanta su da masu arziki, wadanda ke da tarin dukiya ga kuma dimbin bashi. Ita kuwa kungiyar agaji ta Odfam ta kare bincikenta, inda ta yi nuni da cewa, abu ne amfi sauki a kididdige yawan dukiyar attajiran duniya, saboda ba su da yawa, don haka Odfam ta dogara da wannan hujjar.
Abin tambaya shi ne, wadanne mutane ne ke da wannan tarin dukiya?
Bisa la’akari da alkaluman kididdigar yawan al’ummar duniya, wadda ta nuna cewa akwai mutane biliyan bakwai da miliyan 200, to akwai mutum miliyan 72 a rukunin wadannan mutane, wadand A kashi daya cikin 100, wadanda ba dukan su suka mallaki biliyoytin dala ba. Sannan a shekarar 2014, mujallar Forbes ta jero sunayen mutum dubu da 645, wadanda suka mallaki biliyoyin dala, inda Bill Gates ya hau kololuwar jerin mutanen. Daga cikin jerin, kashi 90 cikin 100 duk maza ne, sannan kashi 30 cikin 100 duk Amurkawa ne.
Masanan tsimi da tanadi, wadanda suka hada da Dan Altman da Thomas Piketty, sun yi takamma kan yadda gibin da ke tsakanin masu dukiya da marasa shi ke dakile ci gaban al’umma. Wasu kuwa sun ce, al’amarin yana da alfanu. Sai dai mafi yawan masanan sun dora alhakin yawan fatara da talauci da tashe-tashen hankula a kan dimbin dukiyar da wasu ’yan tsirari suka tattare.