Attajiran kasar nan na shiga kungiyoyin ’yan ta’adda – Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai wasu attajirai a kasar nan da suke shiga kungiyoyin ’yan ta’addda. Farfesa Osinbajo ya ce bayan talakawan da suke shiga kungiyoyin saboda neman abin duniya, akwai wasu attajirai da suke shiga irin wadannan kungiyoyi, inji shi.Babban Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban kasar ta Fuskar Yada Labarai, Laolu […]
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai wasu attajirai a kasar nan da suke shiga kungiyoyin ’yan ta’addda.
Farfesa Osinbajo ya ce bayan talakawan da suke shiga kungiyoyin saboda neman abin duniya, akwai wasu attajirai da suke shiga irin wadannan kungiyoyi, inji shi.
Babban Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban kasar ta Fuskar Yada Labarai, Laolu Akande a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ruwaito Osinbajo yana bayyana hakan lokacin da Jakadan Amurka na Musamman kan Yaki da Ta’addanci Rashad Hussain, ya ziyarce shi a Fadar Shugaban kasa, ranar Litinin.
Sanarwar ta ce “gwamnatin tarayya za ta fito da wani shiri wanda zai hada da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, inda za su yi aiki tare da fatan kawo karshen kungiyoyi kamar Boko Haram”
Mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnati za ta kafa wata cibiya don samar da bayanai game da masu tsauraran akidoji musamman a yankin Arewa-maso-Gabas. Har ila yau, ya ce cibiyar za ta rika bankado munanan ayyukan ’yan ta’adda.