Attajiran Larabawa na yayin motar Tafi-da-gidanka

Hamshakan atttajiran Larabawa na yayin motar tafi-da-gidanta, wadda kudinta ya kai Fam miliyan biyu, wato daidai Dala miliyan uku da dubu 100 (Naira 533,200000)Wannan mota mai tsawon kafa 40, sunanta eleMMent Palazzo, wadda wani kamfanin kasar Austiraliya, Marchi Mobile ya kera, kuma an lullubeta da zinari, an sanya mata kayan alatu, wadanta suka hada da […]

Attajiran Larabawa na yayin motar Tafi-da-gidanka

Motar tafi-da-gidankaHamshakan atttajiran Larabawa na yayin motar tafi-da-gidanta, wadda kudinta ya kai Fam miliyan biyu, wato daidai Dala miliyan uku da dubu 100 (Naira 533,200000)
Wannan mota mai tsawon kafa 40, sunanta eleMMent Palazzo, wadda wani kamfanin kasar Austiraliya, Marchi Mobile ya kera, kuma an lullubeta da zinari, an sanya mata kayan alatu, wadanta suka hada da akwatin talabijin mai fadin inci 40, da wurin shakatawa da kuma dakin kwana. Motar na da wata farfajiyar hutawa a kasan benenta.
Jaridar Dailymail, ta ruwaito cewa, wannan motar da kanta take tsaftace kanta. Don haka hamshakatan attajiran kasashen Larabawa, musamman masu hada-hadar man fetur su ke ta rububin sayen motar, a daukacin fadin Gabas ta Tsakiya.
Wannan motar ta yi daidai da bukatun masu dimbin dukiya, ko mutanen da suka shahara a fadin duniya. Kuma an yi da Wurin zaman direba a motar Mobile Homefenti fari.Dakin shaqatawa a benen motar gidan tafi-da-gidanka

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan