Attajiran ma’aurata sun rubuta biri a matsayin magajinsu

Wasu iyalai attajirai a kasar Indiya sun rubuta biri a matsayin magajinsu, inda suka bayyana cewa, tun daga ranar da suka dauki wannan biri a matsayin dan riko, suka samu yalwar arziki. Don haka su ma ke kokarin ganin rayuwarsa ta inganta ko bayan ransu. Ma’auratan Brajesh Sribastaba da matarsa Shabista, ba su da ’ya’ya, […]

Attajiran ma’aurata sun rubuta biri a matsayin magajinsu
Attajiran ma’aurata sun rubuta biri a matsayin magajinsu

Wasu iyalai attajirai a kasar Indiya sun rubuta biri a matsayin magajinsu, inda suka bayyana cewa, tun daga ranar da suka dauki wannan biri a matsayin dan riko, suka samu yalwar arziki. Don haka su ma ke kokarin ganin rayuwarsa ta inganta ko bayan ransu.

Ma’auratan Brajesh Sribastaba da matarsa Shabista, ba su da ’ya’ya, shi ya sa suke daukar birinsu mai suna Chunmun a matsayin da, don haka suka bude wata gidauniyar da za a yi amfani da ita wajen kula da rayuwarsa ko bayan ransu.
“Mutane za su dauka cewa mun haukace, ta yiwu ma su yi mana dariya, amma mu mun san muhimmancin Chunmun,” a cewar uwargida Shabista, ’yar shekara 45, kamar yadda ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
“Ba mu da ’ya’ya, shi ya sa Chunman ya zama da a gareni. Za mu tabbatar da cewa ko bayan rnamu, rayuwar Chunmun ba ta tagayyara ba, kuma haka zai ci gaba da ryauwa
Wadannan ma’aurata korarru ne daga iyayensu, bayan da suka yi aure ba tare da amincewarsu ba, sun bayyana cewa, sun kasance matalauta, amma da suka riki birin a shekarar 2004, tuni suka kasance cikin yalwar dukiya.
Ma’auratan sun mallaki gidan kansu a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin Indiya, sannan suna filin kasa da tarin dukiya.
Shabista dai lauya ce, kuma maigidanta dan shekara 48 na da harkokin kasuwanci, wadanda suka hada da gidan talabijin na tauraron dan Adam da kamfanin fulawa, wadanda duk an lakaba musu sunan biri Chunmun.
Biri na da daki mai na’urar sanyaya daki a cikin gidan wadannan ma’aurata, ind asuka samar masa mata mai suna Bitti.
Wadannan birai guda biyu suna cin abincin mutanen kasar Sin da shayi da ruwan lemun mangwaro, a cewar Shabista, lokacin da take gudanar da bikin auren biran, in data gayyaci daruruwan kawayenta.
A halin yanzu birin yana da shekara 10, kuma birai na rayuwa a tsakanin shekarun 35 zuwa 40. Bayan rasuwarsa ma’auratan na sa ran za a yi amfani da kudinsa wajen kula da jin dadi da walwalar birai a kasar Indiya, inda ake cin zarafin dabbobi.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume